Mambobi sun yiwa shugaban jam'iyyar APC a jihar Jigawa duka sai da ya kwan Asibiti
- Yayinda ake shirin zaben kananan hukumomi, wasu yan jam'iyya sun yiwa shugabansu ligis
- Wannan ya biyo bayan zargin rashin adalcin da suka yi masa
- Shugaban jam'iyyar mai shekaru 70 a duniya na kwance yanzu a asibiti
Mambobin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a karamar hukumar Dutse na jihar Jigawa, Yakubu Ibrahim. ya sha mumunan duka daga wajen mambobin jam'iyyarsa.
Wannan ya biyo bayan sanarwan gwamna Muhammadu Badaru na sunayen yan takaran jam'iyyar a zaben kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa ranar 26 ga Yuni.
A cewar rahoton PT, sisa jawabin da mai magana da yawun gwamnan, Auwal Sankara yayi, ya ce Bala Chamo aka zaba matsayin dan takaran jam'iyyar na karamar hukumar Dutse.
Amma wasu mambobi jam'iyyar sun ce ba Bala Chamo mafi akasarin jama'ar Dutse suka zaba ba.
Fusatattun matasan sun dira sakatariyar jam'iyyar inda suka fito da shugabansu kuma sukayi masa lilis.
An ruwaito cewa Shugaban jam'iyyar mai shekaru 70 na kwance a asibiti yanzu.
Kwamishanan yan sandan jihar, Usman Gomna, ya bayyanawa manema labarai an damke mutum biyu sakamakon haka.
DUBA NAN: Garba Shehu ya sani cewa shi fa kawai dan aike ne, yayi hattara da kalamansa: Gwamnonin kudu 17

Asali: Twitter
KU KARANTA: Babban Limamim jami'ar UNIMAID zai aurar 'yayansa 10 rana guda
Shugaban yan sandan ya ce sabani aka samu tsakanin 'yayan jam'iyya.
Hukumar gudanar da zabe ta jihar ta shirya zaben kananan hukumomin ranar 26 ga Yuni.
Shugaban hukumar, Adamu Ibrahim. ya bayyana kamfanin dillancin Najeriya NAN a wata hira ranar Lahadi cewa za su shirya zaben lumana da adalci a kananan hukumomi 27 na jihar.
A bangare guda, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa tarihi ba zai wa jam'iyyar APC kyauba idan ta cigaba da ƙona ofisoshin hukumar zaɓe, INEC.
Sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, shine ya bayyana haka a wani jawabi da aka yi wa take da "Har yanzun PDP na zargin APC nada hannu a ƙona ofisoshin INEC"
Hukumar zaɓe INEC tace waɗannan hare-haren da ake kaiwa ofisoshinta zasu iya kawo tsaiko ga zaɓen 2023 dake tafe, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Asali: Legit.ng