Saudi ta kawo tsauraran dokoki 10, ta kayyade wadanda za a ba damar yin aikin Hajji a 2021

Saudi ta kawo tsauraran dokoki 10, ta kayyade wadanda za a ba damar yin aikin Hajji a 2021

Tun bayan da aka samu barkewar annobar cutar COVID-19 a kasashen Duniya, kasar Saudi Arabia ta bada damar ayi aikin hajji a wannan shekarar.

A shafin Haramain, kasar Saudi Arabiya ta bayyana cewa mutane 60, 000 ne za a kyale su gudanar da aikin hajjin shekarar da za ayi a watan Yulin bana.

A jiya ma’aikatar lafiya ta Saudi Arabiya ta bada sanarwar za a ba mutane 45, 000 daga kasashen Duniya kujerun aikin hajji domin su sauke farali a 2021.

Za a bar wa mutanen da ke kasar Saudi ragowar kujeru 15, 000 domin su samu damar yin wannan ibada a shekarar bana, kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

SIASAT ta ce wani jami’in gwamnatin kasar Fakistan, Maulana Tahir Ashrafi ya tabbatar da wannan mataki yayin da ya zanta da gidan talabijin Samaa TV.

KU KARANTA: Saudiyya ta na neman watan Ramadana domin fara azumi

Ga wasu daga cikin sharudan da aka kawo:

1. Maniyyata 60, 000 kadai za su yi aikin hajji a shekarar nan daga kasashen Duniya da kasar Saudi Arabiya.

2. Dole maniyyaci ya zama tsakanin ‘dan shekara 18 zuwa 60.

3. Ya wajaba duk wanda zai yi aikin hajji ya zama cikin koshin lafiya.

4. Dole ya zama wanda zai yi aikin hajji bai kwanta ciwo a asibiti a cikin watanni shidan da suka shude ba.

5. Tilas ne maniyyaci ya yi rigakakafin cutar COVID-19.

6. Dole sai gwamnatin Saudiyya ta san da zaman irin allurar rigakafin da mutum ya yi.

7. Kuma dole ne ace an yi rigakafin farko kafin ko a ranar 1 ga watan Shawwal, 1442 (ranar karamar sallah).

8. Sannan dole ne ace an yi rigakafi na biyu kafin ranar 14 ga watan Shawwal, 1442 (gabanin a shigo Saudi).

Saudi ta kawo tsauraran dokoki 10, ta kayyade wadanda za a ba damar yin aikin Hajji a 2021
Ana aikin Hajji Hoto: www.leadership.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Ba mu gayyatar Yahudawa zuwa kasar mu - Saudi Arabia

9. Ya wajaba a killace maniyyata na tsawon kwanaki uku da zarar sun shigo Saudi Arabiya daga kasar waje.

10. Ya zama dole a rika bada tazara, tare da rufe fuskoki, da bin duk wasu matakan kariya domin a kare lafiyar mahajjata.

Bayan wadannan dokokin da aka shigo da su, akwai wasu ka’idoji dabam da za a bi wajen kai ziyara, ranar hawan Arafah, da shiga cikin harami.

Tun a kwanakin baya kun ji cewa Kasar Saudiyya ta bayyana cewa, dole ne dukkan masu zuwa aikin hajjin bana suyi rigakafin cutar Coronavirus a gida.

Kasar tace allurar rigakafin zata zama daya daga cikin sharruddan shiga kasa mai tsarkin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel