Katobara: Kalamansa sun sa ana hurowa Ministan Buhari wuta ya bar kujerar da yake kai
- Shugabannin kungiyar Southern Leadership Conference sun yi Abubakar Malami raddi
- Kungiyar ta dura kan Ministan bayan ya soki hana kiwon dabbobi a fili a jihohin Kudu
- SLC ta ce babu yadda za a kamanta masu saida karafan mota da masu yin ta’asa a gona
Kungiyar Southern Leadership Conference (SLC) ta yi kira ga Abubakar Malami SAN ya yi murabus daga kan kujerar da yake kai ta Ministan shari’a.
Southern Leadership Conference ta bukaci Ministan kuma babban lauyan gwamnatin tarayya ya bar gwamnati ne a game da wasu kalamai da ya yi kwanaki.
Abubakar Malami ya nuna rashin goyon baya a kan matakin da gwamnonin jihohin Kudancin kasar nan suka dauka na haramta yin kiwon dabbobi a fili.
KU KARANTA: ‘Yan siyasan da za suyi takarar Gwamnan jihar Kano a 2023
Leaership ta ce SLC ta bayyana matsayarta a wani jawabi da ta fitar da ta bakin shugabanninta, Chinedu Karl Uchegbu, Angela Onwaeze da Sokari Goodboy Sokari.
Karl Uchegbu, Onwaeze da Goodboy Sokari sun ce sam ba su yi mamakin yadda Ministan ya kamanta yawo da dabbobi da kuma saida karafunan mota ba.
Jawabin ya ce: “Mu, kungiyar SLC ba muyi mamakin kalaman Ministan shari’a, kuma babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami lokacin da yake adawa da matsayar gwamnonin Kudu na hana yawon kiwon dabbobi ba, ganin yadda ya saba fifita Fulani.”
“AGF ya kamanta haramta kiwon dabbobi a fili da gwamnonin Kudu su kayi da gwamnonin Arewa su hana kasuwancin karafunan motoci a yankin Arewa.”
KU KARANTA: Masu so Gwamnan Kogi ya nemi Shugaban kasa a 2023 sun yi taro
A cewar kungiyar SLC, Ministan ya nuna kabilancinsa a fili, ya saba rantsuwar da ya yi a matsayinsa na babban mai kare gwamnatin tarayya a gaban kotu.
SLC ta ce Abubakar Malami ya jawowa Najeriya abin dariya a cikin sahun kasashen Duniya.
“Babu hankali a hada kiwon dabbobi, ana barnata kayan gonan mutane, da kasuwancin halal na saida karafunan motoci a cikin shaguna.” Inji shugabannin SLC.
Kwanakin baya kun samu labari cewa kakakin Majalisar dattawa, Sanata Ajibola Basiru, ya yi kaca-kaca da Ministan shari’a, ya na so shugaban kasa ya tsige shi
Har ila yau, yunkurin kare makiyayan ya jawo Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ya bi sahun ‘Yan Majalisar, ya soki matsayar da Ministan shari'ar kasar ya dauka.
Asali: Legit.ng