Labari mai zafi: Ana shirin zabe, IPOB sun banka wuta, sun kona ofishin INEC a duhun dare
- Ana zargin ‘Yan IPOB da cinna wuta a ofishin hukumar INEC a Anambra jiya
- Bayan nan ‘Yan bindigan sun kai wa wasu tawagar ‘Yan Sanda hari a Awka
- An yi wannan ta’asa ne a lokacin da ake ta shirin gudanar da zaben gwamna
Hukumar gudanar da zabe na kasa, INEC ta sake gamu wa da cikas a lokacin da ta ke koka wa a kan matsalar tsaro, inda aka kona wani ofishinta.
A cikin daren Litinin, 24 ga watan Mayu, 2021, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, ofishin INEC na jihar Anambra da ke garin Awka ya na ci da wuta.
Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin ‘yan kungiyar IPOB masu rajin samar da kasar Biyafara ne suka yi wannan aiki, su ka sa wa ofishin wuta.
KU KARANTA: Hadarin jirgi ya yi sanadiyyar mutuwar COAS, Janar Ibrahim Attahiru
Wadannan ‘yan bindiga sun burma cikin babban ofishin INEC mai zaman kanta, suka cinna wuta bayan cin karfin jami’an ‘yan sanda da suke wurin.
Jaridar ta ce ‘yan bindigan na kungiyar Independent People of Biafra sun yi ta faman ba-ta-kashi da ‘yan sanda, aka yi musayar wuta a a daren na jiya.
‘Yan bindiga sun yi wannan danyen aikin ne a lokacin da ake lissafin saura watanni biyar rak INEC ta gudanar da zaben sabon Gwamna a Anambra.
Daga lokacin da IPOB ta fara wannan ta’adi, ta kona ofisoshin hukumomi da gwamnati da-dama.
KU KARANTA: Shugaban EFCC ya ce sun gano N1bn a asusun wani ma'aikaci
Jaridar Vanguard ta ce bayan ofishin INEC, ‘yan bindigan sun auka wa wani ofishin ‘yan sanda a garin Awka, An kai harin ne da kimanin karfe 8:00 na dare.
‘Yan bindigan sun zo ne a cikin wata mota kirar Hilux, suka shiga buda-wuta a kan titi kafin su isa zuwa ofishin INEC, hakan ya sa mutane duk suka tsere.
Jami’in REC na jihar Anambra, Dr. Nkwachukwu Orji, ya ce ya samu labarin an kawo masu hari, amma bai iya bada wani cikakken bayani ba a cikin daren.
Kafin nan an ji shugaban hukumar INEC ya na kukan cewa an kona ofishinsu 21 a fadin Najeriya, wanda hakan zai iya kawo cikas a zabe mai zuwa na 2023.
A dalilin haka ne hukumar INEC ta shirya wani zama na musamman da shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya da duk manyan kwamishinoni zabe na kasa.
Asali: Legit.ng