Kana bata sunan Gwamnati – Sanatoci sun taso Ministan Buhari ya sauka daga kujerar da yake kai

Kana bata sunan Gwamnati – Sanatoci sun taso Ministan Buhari ya sauka daga kujerar da yake kai

- Abubakar Malami ya soki hana Makiyaya kiwo a fili da aka yi a jihohin Kudu

- Mai magana da yawun Sanatoci ya maidawa Ministan martani ranar Alhamis

- Shi ma Gwamnan Ondo yayi Allah-wadai, yace ba za su janye matakin nan ba

Mai magana da yawun bakin majalisar dattawan Najeriya, Ajibola Basiru, ya ce Abubakar Malami ya na bata wa gwamnatin Muhammadu Buhari suna.

Jaridar The Cable ce ta rahoto Sanata Ajibola Basiru, ya na wannan bayani a matsayin raddi ga Ministan shari’a, kuma babban lauyan gwamnati, AGF.

A wani jawabi da ya fitar a ranar Alhamis, 20 ga watan Mayu, Ajibola Basiru, ya ce babu dalilin da Abubakar Malami SAN zai cigaba da rike kujerar Minista.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin ministan shari'a, Abubakar Malami SAN

Kakakin Sanatocin kasar ya ce aikin AGF shi ne hada-kan al’ummar Najeriya, ba kokarin raba su ba.

Ya ce: “Duk wanda ba zai iya ajiye son kabilarsa ba, bai kamata a damka masa amana ba, musamman a wannan lokaci da ake kiraye-kirayen a barke.”

Sanatan ya yi tir da yadda Ministan ya fito ya na wasu kalamai inda yake sukar haramta kiwon dabbobi a fili a Kudu, a matsayinsa na mai kare gwamnati.

“Irin wadannan kalamai suka sa aka maida Najeriya abin dariya a sahun kasashe, ana cin mutuncin gwamnatin Muhammadu Buhari.” Inji Basiru.

KU KARANTA: An cin ma yarjejeniya a kan yajin-aikin NLC jihar Kaduna - Minista

Kana bata sunan Gwamnati – Sanatoci sun taso Ministan Buhari ya sauka daga kujerar da yake kai
AGF, Abubakar Malami Hoto: @MalamiSAN
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ce shi ma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu wanda babban lauya ne irin Abubakar Malami, ya soki Ministan, ya fada masa ya je kotu.

A wani jawabi da gwamnan ya fitar a jiya, ya ce maganar hana makiyaya yawo da dabbobi a kudancin Najeriya da sunan kiwo tana nan, ba za a janye ba.

Akeredolu ya ce abin takaici ne babban lauya ya rika wadannan kalamai, yayi Allah-wadai misalin da Ministan ya bada, yace cike yake da jahilci da girman-kai.

A jiya kun ji cewa Ministan shari'a na ƙasa, Abubakar Malami, ya gargaɗi gwamnonin kudancin Najeriya a kan matakin da suke shirin ɗauka na hana kiwo.

Malami yace Najeriya tana da kundin tsarin mulkin da take aiki da shi, kuma ya ba kowane ɗan Najeriya yancin yawo a faɗin ƙasar nan duk yadda ya ga dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel