Za mu dauki dawainiyar mutum 4 daga jihohi 36 da Abuja su yi karatun Jami’a inji Kwankwaso

Za mu dauki dawainiyar mutum 4 daga jihohi 36 da Abuja su yi karatun Jami’a inji Kwankwaso

- Kwankwasiyya Development Foundation za ta ba yara karatun Jami’a

- Gidauniyar ta ce a wannan karon za ta dauki mutane daga kowace jiha

- Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya bada wannan sanarwar

Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya bada sanarwar gidauniyarsu za ta cigaba da abin da ta saba na ba matasa ilmi.

A wata hira da aka yi da Sanata Rabiu Kwankwaso a gidan rediyo, ya bayyana cewa gidauniyar Kwankwasiyya za ta sake tura wasu matasa makaranta.

Wani babban masoyin ‘dan siyasar wanda ya yi wa kansa lakabi da Kwankwason Twitter, ya fito da wannan labari a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi.

KU KARANTA: Kwankwaso ya saida kadarorinsa domin Talaka ya je Makaranta

Wannan karo gidauniyar Kwankwasiyya Development Foundation za ta zabi wasu matasa da za a ba damar yin karatu a sabuwar jami’ar Mewar a Abuja.

Jami’ar Mewar ta kasar Indiya ta shigo Najeriya don haka wannan karo Kwankwasiyya Development Foundation ta zabi ta kai yara zuwa can.

An raba kujerun da za a bada tsakanin mata da maza, sannan za a dauko mutum hudu daga kowace jiha da ke Najeriya da kuma babban birnin tarayya.

Tsohon gwamnan ya yi albishiri, ya ce: “Akwai jami’a ta kasar Indiya, wanda wasu da yawa daga cikinku kun santa, jami’ar Mewar ta shigo Najeriya yanzu.”

KU KARANTA: Siyasar Kano: Rikicin cikin gida ya shiga tafiyar Kwankwasiyya

Za mu dauki dawainiyar mutum 4 daga jihohi 36 da Abuja su yi karatun Jami’a inji Kwankwaso
'Yan makaranta Hoto: @Noble_Hassan
Asali: Twitter

“Saboda maganganu na ‘Yan Kwankwasiyya a Najeriya, ‘Ayi-ayi, ya aka yi jihar Kano kawai ake yi wa? Muma a samu a ciki’....” inji fitaccen ‘dan siyasar.

“Saboda matsaloli na waje, yanzu mun yi tsari, gidauniyar Kwankwasiyya Foundation za ta ba kowace jiha ta Najeriya da birnin Abuja, maza biyu da mata biyu.”

Sanata Rabiu Kwankwaso yake cewa za su yi tsari na yadda za a ba masu mabukata wannan dama.

Idan za ku tuna, a 2019, gidauniyar nan ta Kwankwasiyya Foundation ta nemi gudumuwar kudi domin aika wasu 'Yan jihar Kano zuwa jami’o’i a waje.

Sanata Rabiu Kwankwaso da dinbin manyan mutane sun halarci wannan biki. Attajirai da manyan ‘yan kasuwa sun tara makudan miliyoyi a taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel