Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ranar birne Janar Attahiru da sauran sojin da suka rasu
- Rundunar sojin Najerya tace an shirya jana'iza tare da birne marigayin COAS a ranar Asabar
- Za a yi jana'izarsa a masallacin kasa dake Abuja tare da sauran hafsohin sojin 6 da suka rasu
- Daga nan za a birnesu a makabartar sojojin Najeriya dake Abuja da karfe 1 na rana
An shirya birne marigayi shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sojoji shida da suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin sama a Kaduna a ranar Asabar, 22 ga watan Mayun 2021, Vanguard ta ruwaito.
A wata takarda da mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yerima ya fitar, ya ce "Za a yi jana'izar a masalallacin kasa da kuma cibiyar kiristoci ta kasa a Abuja.
"Za a yi jana'izar marigayi COAS da manyan sojin shida tare da birnesu a makabartar sojoji ta kasa dake Abuja da karfe daya na rana.
"A wani bangare, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi ya kwatanta rasuwar da abun alhini kuma mara dadi ganin cewa watanni hudu kacal shugaban yayi a kan kujerar mulkin."
KU KARANTA: Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba game da kungiyar ISWAP
A sakon ta'aziyyar da Janar Magashi ya mika, ya ce hatsarin jirgin saman da ya lakume rayuwar shugaban sojin kasan tare da hadimansa babban lamari ne.
Yayin ta'aziyya ga kwamandan sojojin Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari, rundunar soji da 'yan Najeriya, ya kwatanta Attahiru da zakakurin soja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin yi wa kasarsa ta gado aiki.
Ya tuna kokarin da ya nuna yayin da yake daraktan hulda da jama'a, kwamandan Operation Lafiya Dole da kuma kwamandan GOC wanda hakan ya kai shi har shugaban rundunar sojin kasa a watan janairun wannan shekarar.
Ya kwatanta zamansa shugaban sojin kasan Najeriya a wannan lokacin da matsalar tsaro ta yawaita da alamar hazaka amma sai wa'adin mulkinsa bai yi tsawo ba.
KU KARANTA: Dalla-dalla: Yadda Shekau ya sheka lahira tare da wasu kwamandojin ISWAP
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasar Najeriya bayan tafiyar da yayi domin halartar muhimmin taro a birnin Paris na kasar Faransa, kamar yadda hadimin shugaban kasan Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Shugaban kasan ya iso kasar wurin karfe 5:15 na yammacin ranar Alhamis inda ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake garin Abuja.
Idan zamu tuna, Buhari ya sauka garin Abuja a ranar Lahadi zuwa birnin Paris, inda ya kwashe kwanaki hudu domin halartar gagarumin taron farfado da tattalin arzikin Afrika bayan annobar Korona.
Asali: Legit.ng