Ba ma gayyatar Yahudawa zuwa kasar Saudi Arabia – gwamnatin Saudiyya

Ba ma gayyatar Yahudawa zuwa kasar Saudi Arabia – gwamnatin Saudiyya

Gwamnatin kasar Saudiyya ta bayyana cewa Yahudawa yan kasar Isra’ila ba su da wuri a kasar Saudiyya, don haka ba sa gayyatarsu, kamar yadda ministan harkokin kasashen waje na Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan ya bayyana.

Ministan ya bayyana haka ne a matsayin raddi ga jawabin ministan cikin gida na kasar Isra’ila wanda a ranar Lahadi yace Yahudawan kasar Isra’ila da Musulman kasar na da hakkin zuwa kasar Saudi Arabia don gabatar da ibada ko kasuwanci.

KU KARANTA: Zazzabin cutar lassa: Likitoci 7 da ma’aikatan jinya 5 na cikin tsaka mai wuya a jahar Adamawa

Amma ministan Saudiyya ya mayar masa da martani da cewa ba zasu taba maraba da yan kasar Isra’ila ba. “Tsarinmu bai canza ba, bamu da wata alaka da Isra’ila don haka duk wani mai amfani da fasfon kasar Isra’ila ba zai shiga kasarmu ba.”

Ba Saudiyya kadai ba, yawancin kasashen larabawa basu da wata alaka da kasar Israila, illa kasashen Misra da Jordan, kuma babban abin da ya lalata alaka tsakaninta da kasashen larabawa shi ne cigaba da kuntata ma Musulman Falasdinawa tare da mamaye yankinsu.

Sai dai Yarima Farhan ya bayyana ma gidan talabijin na CNN cewa: “Muna kira tare da bada kwarin gwiwa da samar da sulhu a rikicin Falasdinawa da Yahudawa, idan har aka samu wannan sulhun, zamu iya duba bukatar kasar Israila na neman kulla alaka da mu.”

A wani labari kuma, mutane uku ne suka rasa ransu a yayin wani kazamar rikicin kabilanci daya barke tsakanin al’ummar Fulani da kabilun Tibabe a kauyen Pangari na karamar hukumar Bali na jahar Taraba.

Wani mazaunin garin mai suna Pius Gura ya bayyana cewa wani bafulatani ne ya shiga gonar wani manomi dan kabilar Tibi mai suna Dooior James, tare da shanunsa, amma a lokacin da manomin ya nemi a biyashi barnar da shanun suka yi masa, sai bahillacen ya kashe shi.

Bayan yan uwan manomi Dooir sun samu labarin abin day faru ne sai suka tattara kansu, inda suka kai ma bahillacen harin ramuwar gayya, suka kashe shi, daga nan ne lamari ya ta’azzara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel