Wasu tsageru sun hallaka jami'an tsaro 2 a Anambara, sun kwashe makamai
- Yan bindiga na cigaba da kaiwa jami'an tsaro hari a yankin kudu maso gabas
- Hakazalika ana cigaba da kona ofishohin hukumar INEC
- Ana tsoron da kamar wuya a samu gudanar da zaben 2023 idan haka ya cigaba
Wasu yan bindiga a daren Juma'a sun hallaka jami'ar hukunar NSCDC biyu a Nneyi, dake karamar hukumar Anambra East inda suka kona motarsu tare da kwashe makamai.
Wata majiya ta bayyana cewa yan bindigan sun kai hari ofishin Nneyi ne suna harbin kan mai uwa da wabi kuma jami'ai biyu suka mutu sakamakon haka.
Kakakin hukumar na jihar, Okadigbo Edwin ya tabbatar da labarin a jawabin da ya saki a Awka, babbar birnin jihar Anambra, rahoton Daily Trust.
"Jiya 21 ga Mayu 2021, misalin karfe 16:35hrs, wasu tsageru sun kai hari mazaunar Sibil Defens dake Nneyi Umueri a karamar hukumar Anambra East, inda suka far harbi," Kakakin yace.
"Hafsoshin dake wurin sun yi musayar wuta da su. A karshe jami'an hukumar biyu sun samu raunuka kuma suka rasa rayukansu."
"Abin takaici, an kwace makamansu bayan bankawa mota wuta," ya kara.
KU KARANTA: Amurka, Burtaniya Sun Bayyana Jimamin Su Kan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru

Asali: Twitter
KU KARANTA: Akalla sau 6 ya zo Borno, ya lashi takobin kawar da Boko Haram: Zulum ya yi jimamin rashin Attahiru
A karshe, ya bayyana cewa kwamandan hukumar na jihar, David Bille, ya shirya kaddamar da bincike tare da sauran hukumomin tsaro don sanin cikakken abinda ya faru.
A bangare guda, gamayyar jami'an hukumar Sojojin Najeriya da na yan sanda a karamar hukumar Kontagora sun ragargaji yan bindiga akalla guda bakwai a cikin daji a jihar Neja.
PRNigeria ta tattaro cewa kwamandan 311 Artillery, T.O Olukukun, da kwamandan yan sandan, Haruna Adamu Swapo ne suka jagoranci farkamin da aka kaiwa yan bindigan.
Yan bindigan na guduwa nee bayan harin da suka kai gonar Sarkin Kontagora a kauyen Masuga kuma suka hallaka 'dansa, Sardaunan Kontagora, Alhaji Bashir Namaska.
Asali: Legit.ng