Bamu ce yan Najeriya su mika mana lambobin IMEI dinsu ba, da kanmu zamu dauka, inji NCC
- Hukumar NCC ta yi fashin baki kan lamarin IMEI
- Wannan ya biyo bayan hada NIN da SIM da aka wajabtawa yan Najeriya yi
- Yan Najeriya sun lashi takobin cewa ba zasu taba baiwa gwamnati lambar IMEI dinsu ba
Hukumar sadarwan Najeriya NCC ta barranta kanta daga rahotannin dake cewa nan da watan Yuli za'a bukaci yan Najeriya su gabatar da lambar IMEI na wayoyinsu.
IMEI wani abu me lambobi 15 da akayiwa kowace waya. Za'a iya amfani da shi wajen bibiyar waya duk inda take.
Diraktan hulda da jama'a na hukumar, Dr. Ikechukwu Adinde, ya saki jawabi da yammacin Juma'a cewa sam hukumar bata ce yan Najeriya su bada lambar IMEI dinsu ba.
Hukumar tace kawai tana shirin amfani da wata na'ura ne wajen dakile sace-sacen waya da kuma kawar jabun wayoyi.
A cewarsa, wannan na'urar za ta dauki lambar IMEI da kanta ba tare da mutum ya mikawa hukumar ba.
DUBA NAN: Sauya shekar gwamna Ayade zuwa APC ya girgiza mu kuma ya bamu kunya, Gwamnan Taraba
KU KARANTA: FG ta yi sulhu tsakanin Kwadago da El-Rufa'i, an yi yarjejeniya
Wani sashen jawabin yace: "Hukumar NCC ta samu labarin da wasu kafafen yada labarai ke cewa hukumar zata fara wajabtawa yan Najeriya mika lambar IMEI na wayoyinsu fari daga Yulin 2021."
"Ko kadan hukumar bata saki wannan jawabi ba kuma ba tada shirin yin hakan."
"Abinda hukumar ke shirin yi shine amfani da wata na'ura ta DMS wacce zata rika kare mutane daga barayin waya da kuma gano jabun wayoyi."
"Na'urar da kanta zata dauki IMEI ba tare da sai mutum ya mika ba."
A baya mun kawo muku cewa hukumar NCC tace fari daga watan Yuli, za'a wajabtawa yan Najeriya gabatar da lambobin IMEI na wayoyinsu.
NCC ta lissafa amfanin wannan abu da take shirin yi
Ya hada da :
1. Domin dakile sayar da jabun wayoyi
2. Domin dakile sace-sacen waya
3. Domin inganta tsaron kasa
4. Domin kare mutuncin kwastamomi
5. Domin samawa gwamnati kudin shiga
6. Domin rage garkuwa da mutane
7. Domin rage amfani da waya sata wajen aikata laifuka
8. Domin dode wayoyin sata
Asali: Legit.ng