Bayan hada NIN da SIM, FG zata fara wajabtawa yan Najeriya mika lambobin IMEI na wayoyinsu

Bayan hada NIN da SIM, FG zata fara wajabtawa yan Najeriya mika lambobin IMEI na wayoyinsu

- Gwamnatin Najeriya ta sanar da wani sabon abu da yan Najeriya zasu mikawa gwamnati na wayoyin salulansu

- Fari daga watan Yuli, za'a bukaci yan Najeriya su mikawa ma'aikatan sadarwar lambobin IMEI na wayoyinsu

- A cewar NCC, wannan zai taimaka wajen inganta lamarin tsaro, dakile satar waya, dss

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta sanar da cewa fari daga watan Yuli, za'a wajabtawa yan Najeriya gabatar da lambobin IMEI na wayoyinsu.

A cewar Punch, wannan na kunshe ne cikin tsarin da hukumar ta shirya na amfani da waya a Najeriya.

Legit ta fahimci cewa wannan na cikin tsare-tsaren da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu.

Wani sashen tsarin yace: "Shugaba Muhammadu Buhari GCFR ya bada umurnin cewa an dabbaka dokar bibiyan wayoyi cikin watanni uku."

IMEI wani abu me lambobi 15 da akayiwa kowace waya. Za'a iya amfani da shi wajen bibiyar waya duk inda take.

DUBA NAN: Sauya shekar gwamna Ayade zuwa APC ya girgiza mu kuma ya bamu kunya, Gwamnan Taraba

Bayan hada NIN da SIM, FGzata fara wajabtawa yan Najeriya mika lambobin IMEI na wayoyinsu
Bayan hada NIN da SIM, FGzata fara wajabtawa yan Najeriya mika lambobin IMEI na wayoyinsu
Asali: UGC

Dalilin da yasa aka dauki wannan mataki

NCC ta lissafa amfanin wannan abu da take shirin yi

Ya hada da :

1. Domin dakile sayar da jabun wayoyi

2. Domin dakile sace-sacen waya

3. Domin inganta tsaron kasa

4. Domin kare mutuncin kwastamomi

5. Domin samawa gwamnati kudin shiga

6. Domin rage garkuwa da mutane

7. Domin rage amfani da waya sata wajen aikata laifuka

8. Domin dode wayoyin sata

DUBA NAN: FG ta yi sulhu tsakanin Kwadago da El-Rufa'i, an yi yarjejeniya

Ra'ayin Masana

Wani masani wanda yake taya hukumar yan sanda bibiyan wayan sata yace za'a iya amfani da IMEI wajen bibiyan wayan sata.

Mutumin wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace: "IMEI na taimakawa wajen samun bayanan waya, wadanda aka kira da waya kullum da kuma adireshin wadanda sukayi amfani da wayar."

Ya ce duk da cewa akwai wadanda ke kokarin canza IMEI na waya, akwai hanyar gano sahihin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel