EFCC: Mun bankado sama da Naira Biliyan 1 daga hannun wani Ma’aikacin Gwamnati

EFCC: Mun bankado sama da Naira Biliyan 1 daga hannun wani Ma’aikacin Gwamnati

- An samu wasu Naira biliyan daya a akawun din wani Ma’aikacin gwamnati

- Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana wannan a jiya

- Abdulrasheed Bawa ya yi wannan bayani a Basa'ilin da ya je majalisar dattawa

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta ce ta samu Naira biliyan 1 daga hannun wani ma’aikacin gwamnati.

Daily Trust ta ce a ranar Alhamis, 20 ga watan Mayu, 2021, hukumar ta bada wannan sanarwar.

Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya yi wannan bayani a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin tattalin arziki na majalisar tarayya.

KU KARANTA: Yadda mu ka yi da Ibrahim Magu - Sabon shugaban EFCC

Abdulrasheed Bawa ya halarci zaman kwamitin ne a dalilin binciken da ake yi game da kudin shigan da ma’aikatun gwamnatin tarayya suke samu.

Majalisar dattawa na binciken kudin da cibiyoyi da ma’aikatun gwamnati suka tattara da 1% da ake biya a matsayin kudin hatimi, daga 2014 zuwa 2020.

Sai dai Abdulrasheed Bawa bai bayyanawa ‘yan majalisar sunan wannan ma’aikacin gwamnati da aka karbe wadannan makudan kudi daga hannunsa ba.

“Akwai kafofi da muke ta toshe wa, ba batun samun kudin shiga ba ne kurum. Mun gano fiye da biliyan daya a asusun wani ma’aikacin gwamnati makon jiya.”

KU KARANTA: Sabon shugaban hukumar EFCC, ya fadi abin da zai iya sa ya ajiye aiki

EFCC: Mun bankado sama da Naira Biliyan 1 daga hannun wani Ma’aikacin Gwamnati
Abdulrasheed Bawa a gaban Majalisa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Da yake bayani a gaban majalisar kasar, Bawa ya jinjina wa Sanatocin kan wannan bincike da suke yi, ya ce da bukatar a toshe duk wata gaba da ake barna.

“Bayan lura da abin da kuke yi, da yadda kwamitinku yake bincike, ina farin ciki da abin da ke faru wa a nan, cigaba ne da kwamitin nan ke wannan aiki.”

A karshe Bawa ya fada wa Sanatocin zai so a ce ya samu rahoton binciken, idan sun karkare aikinsu.

A makon nan ne aka ji Shugaba Buhari Muhammadu Buhari yana cewa ya san zafin sha kasa a zabe, don haka ya dage a kan sai ya inganta zabukan Najeriya.

Shugaban Najeriyar ya ce a 2019, APC ta rasa wasu jihohi, hakan ya nuna adalcin gwamnatinsa. Buhari ya yi wannan jawabi yayin da yake Faris, kasar Faransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel