FG: Za mu nada kwamitin mutane 10 da za su yi wa Gwamnatin El-Rufai da Kungiyar NLC sulhu

FG: Za mu nada kwamitin mutane 10 da za su yi wa Gwamnatin El-Rufai da Kungiyar NLC sulhu

- Wakilan Gwamnatin Kaduna sun fara zama da Jagororin kungiyar Kwadago

- Ministan kwadago ya ce za a kafa kwamiti ya kawo karshen rikicin da ake yi

- Sanata Chris Ngige ya bayyana cewa kowane bangare ya maida kayan fadansa

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamitin mutane 10 da zai yi aikin shawo sabanin da ke tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin jihar Kaduna.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa hakan na zuwa ne bayan jami’an gwamnatin Kaduna sun zauna da wakilan kungiyar kwadago ta kasa a garin Abuja.

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi alkawarin za ta daina tsangwamar ma’aikatanta, sannan ta amince za a samu kyakkyawar dangantaka tsakaninta da su.

KU KARANTA: El-Rufai ya zargi sauran Gwamnoni da juya masa baya a rikicinsa da NLC

Ministan kwadago na kasa, Sanata Chris Ngige, ya yi wa ‘yan jarida jawabi bayan wannan taro, yace za su duba abubuwan da suka jawo wa bangarorin sabani.

Ministan ya ce kwamitin da aka kafa yana da wakilai daga bangaren ‘yan kwadago da gwamnatin Kaduna, kuma za su yi la’akari da dokokin kwadago.

Chris Ngige ya ce: “Taron ya nuna an samu matsalar sadarwa ne tsakanin gwamnatin jiha da NLC.”

“Saboda haka mun kafa kwamitin mutum 10, mai dauke da wakilai 6 daga gwamnatin jiha, 3 aga kungiyar NLC, domin a zauna, a samu mafita.” Inji Sanata Ngige.

FG: Za mu nada kwamitin mutane 10 da za su yi wa Gwamnatin El-Rufai da Kungiyar NLC sulhu
Malam Nasir El-Rufai Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: An ba El-Rufai kwana 2 ya dawo da wadana ya kora daga aiki

Bangaren gwamnatin Kaduna zai fito da shugaban wannan kwamiti, sannan mataimakin shugaban kungiyar NLC na kasa ne zai zama mataimakinsa.

Minista ya ce an cin ma yarjejeniya cewa ba za a sake shiga wani yajin-aiki ba, haka zalika gwamnatin Kaduna ba za ta sake tsangwamar wani ma’aikaci.

Vanguard ta ce Najeem Usman, Omoabie Akpan, da Aloy Muoneke da wasunsu sun halarci zaman. Amma gwamna Nasir El-Rufai bai samu halarta ba.

Idan za ku tuna, kwamishinan kananan hukumomi, Jafaru Sani da shugaban ma’aikatan gwamnatin Kaduna, Bariatu Mohammed, sun zauna da ‘Yan NLC.

Bangaren gwamnati da ‘yan kwadago a karkashin jagorancin Kwamred Ayuba Wabba, sun sa hannu a wata yarjejeniyar MOU a zaman a suka yi a birnin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel