Jigon Jam’iyya ya ce APC ta mutu murus, ya fadi ranar da za ayi mata jana’iza a Najeriya

Jigon Jam’iyya ya ce APC ta mutu murus, ya fadi ranar da za ayi mata jana’iza a Najeriya

- Akwai yiwuwar kwamitin rikon kwarya na APC zai daga zaben shugabanni

- Wasu suna ganin wannan dage-dage da ake yi zai iya jawo baraka a jam’iyya

- Lekan Ojo ya na ganin ta kare wa APC, sai dai kurum a jira ranar jana'izar ta

Akwai surutun da ake yi a APC kan shirin da wasu manyan jam’iyya suke yi na kara wa’adin kwamitin rikon kwarya da ke karkashin Alhaji Mai Mala Buni.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yunkurin sabunta wa’adin kwamitin Mai Mala Buni zuwa bayan watan Yuni, zai iya haifar da wani rikici a jam’iyyar APC.

A watan Yunin 2020 ne aka rantsar da shugabannin rikon kwarya, aka ba su tsawon watanni shida su jagoranci jam’iyyar zuwa ga zaben shugabanni na kasa.

KU KARANTA: Ana neman wasu shugabannin PDP kan zargin satar N10b

A karshen Disamban bara wannan wa’adi ya zo karshe, don haka majalisar NEC ta kara wa Mala Buni watanni shida, da sa ran zai karkare aikin da aka ba shi.

A halin yanzu saura kwanaki kusan 40 kacal suka rage wannan wa’adin ya cika, Vanguard ta ce babu alamun jam’iyyar APC za ta kira taron gangaminta na kasa.

Daya daga cikin manyan jam’iyyar APC, Barista Abdullahi Jalo, ya bayyana cewa za a iya fuskantar matsala ta fuskar shari’a idan aka gaza shirya zaben.

Abdullahi Jalo ya ce: “Babban gangamin jam’iyya ba wasa ba ne, abin da nake tsoro kenan. Dole ne a kira wannan taron, idan ba ayi a watan Yuni ba, akwai matsala.”

Jigon Jam’iyya ya ce APC ta mutu murus, ya fadi ranar da za ayi mata jana’iza a Najeriya
Taron APC NEC Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Za a tursasawa Shugaban kasa nada Ministoci wata 1 da hawa mulki

Wani jigon APC a kudancin Najeriya, Lekan Ojo, ya tabbatar da cewa ‘ya ‘yan APC da-dama sun zura idanu ne, suna jiran ganin yadda lamarin zai kasance.

Cif Ojo ya soki aikin da kwamitin rikon kwaryar yake yi, ya ce bangare guda na APC ake jawo wa. Ojo ya ce ba za a kai labari ba, shiyasa aka gaza kiran taron.

“Saboda haka jam’iyyar ta mutu; APC ta mutu. Shiyasa ake ta wasa da hankali ana daga zaben kullum. Duk ranar da aka kira zaben, ranar za a birne gawar APC.”

Tun a ranar Litinin, jaridar Punch ta rahoto sakataren kwamitin rikon kwarya na APC, Sanata John James Akpanudoedehe, yana cewa ba a sa lokacin yin zabe ba.

Sanata John James Akpanudoedehe ya ce masu yada jita-jitar za a fito da jadawalin zaben shugabanni, wasu ne kurum da ke fake wa da sunan 'yan jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel