Gwamna Bello ya tabbatar da labari maras dadi, ‘Yan bindiga sun aika Sojoji barzahu

Gwamna Bello ya tabbatar da labari maras dadi, ‘Yan bindiga sun aika Sojoji barzahu

- ‘Yan bindigan da suka addabi mutanen Neja, sun harbe wasu Sojojin kasa

- Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce an yi asarar sojoji uku a garin Mariga

- Amma an yi nasarar fara dawo da wadanda su ke sansanin IDP zuwa gida

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce sojoji uku sun mutu a hannun ‘yan bindiga a karamar hukumar Magama da ke jihar ta Neja.

Jaridar Premium Times ta rahoto gwamna Abubakar Sani Bello ya na cewa an yi nasarar hallaka wasu daga cikin wadannan miyagun ‘yan bindiga.

Gwamnan Neja ya kuma tabbatar da cewa an gano gawan biyu daga cikin sojojin a lokacin da jami’an tsaro suka bi ‘yan bindigan da suka kai harin.

KU KARANTA: Mutuwar Shekau ishara ce ga masu tada kafar baya - Adamu Garba

Mai girma gwamnan ya yi wannan bayani ne sa’ilin da yake magana da manema labarai bayan ya yi taro da shugabannin hafsoshin tsaro a garin Minna.

Kamar yadda sakataren yada labaran gwamnan Neja, Mary Noel-Berje, ta bayyana a ranar Talata, wasu da aka fatattaka sun fara koma wa garuruwansu.

Mary Noel-Berje ta ce: “An fara samun sa’ida a kauyukan da ‘yan bindiga suka fatattaki al’umma a yankin Shiroro, Munya, da karamar hukumar Mariga.”

“Al’umma daga kauyuka 25 da aka tada suna koma wa ainihin gidajensu.” Inji jami’ar gwamnatin.

KU KARANTA: China ta zargi Amurka da ba Israila da makaman kashe Falastinawa

Gwamna Bello ya tabbatar da labari maras dadi, ‘Yan bindiga sun aika Sojoji barzahu
Gwamna Sani Bello Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

“Ina farin cikin sanar da ku cewa an samu cigaba sosai, ‘yan gudun hijita da-dama sun koma kauyukansu, musamman a Shiroro, Munya da Mariga.”

Gwamna Bello ya kara da cewa idan da gwamnatin tarayya za ta baza jami’an sojoji a jihar, za a kara samun nasara, ya na mai tsoron za ayi fatarar abinci.

Jaridar The Nation a wani rahotonta, ta tabbatar da hare-haren da aka kai a karamar hukumar Mariga, ta ce a sanadiyyar haka an rasa wasu sojojin kasa.

Dazu mu ke ji cewa 'dan Sarkin Kontagora, Bashar Saidu Namaska, yana cikin mutanen da 'yan bindiga suka hallaka yayinda suka kai hari gonar Mai martaba.

'Dan Sarkin ya na tare da wasu mutane ne cikin gonar dake titin zuwa Zuru a lokacin da yan bindiga suka kai musu farmaki a ranar Talatar nan da yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel