Kasar China ta fasa-kwai, ta ce Amurka ke hura wutar rikicin mutanen Falastina-Isra’ila

Kasar China ta fasa-kwai, ta ce Amurka ke hura wutar rikicin mutanen Falastina-Isra’ila

- Sin ta ce Amurka ta na taimakawa wajen hura wutan rikicin da ake yi a Gaza

- Kasar ta yi tir da matakin da Amurka ta dauka, na kin Allah-wadai da Isra’ila

Kasar Sin tana zargin Amurka da taimakawa da goyon baya a rikicin da ake yi a gabas ta tsakiya, inda Isra’ila take muzgunawa mutanen Falastina.

Press TV ta fitar da rahoto cewa Sin tana ganin laifin kasar Amurka wajen hura wutan rikicin.

Mai magana da yawun bakin ma’aikatar harkokin kasar wajen Sin, Zhao Lijian, ya yi wannan bayani a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida a Beijing.

KU KARANTA: Isra'ila ta rusa gidan jaridar Aljazeera a Gaza

Da yake magana a ranar Talata, 18 ga watan Mayu, Mista Zhao Lijian, ya ce gwamnatin Joe Biden ta amince ta saida wa Isra’ila makaman fam $735m.

Da wadannan makamai ne kasar Isra’ila ta ke cigaba da mamaye Falastina daga yankin zirin Gaza.

Lijian yake cewa a taron majalisar dinkin Duniya da aka yi na ranar 16 ga watan Mayu, akasarin kasashen majalisar tsaro sun amince a tsagaita wutan yaki.

Babban jami’in kasar Sin ya ce mafi yawan kasashe suna goyon bayan a samu mafita domin a kawo karshen azabtar da mutanen kasar Falastina suke yi.

KU KARANTA: ‘Yan Yahoo-Yahoo sun yi zanga-zanga a kan ‘cin-kashin’ da EFCC ta ke yi masu

Kasar China ta fasa-kwai, ta ce Amurka ke hura wutar rikicin mutanen Falastina-Isra’ila
Shugabannin Amurka, Israila, Falastina Hoto: www.nbcnews.com/politics
Asali: UGC

A karo na uku, Amurka ta ki bada damar a fitar da dunkulallen jawabi da sunan majalisar tsaron majalisar dinkin Duniya, ta hana a tsagaita wuta a yankin.

Majalisar dinkin Duniya ta yarda a kawo zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, amma Amurka tana hura wutar rigimar ne a maimakon ta kashe.” Inji Lijian.

Zhao Lijian ya ce: “Amurka ta ware kanta ita kadai a majalisar UNSC. Ta saba wa koken da kowa yake yi. Duniya tana Allah-wadai da abin da kasar Amurka ta yi.”

Jami’in kasar ta Sin ya ce Amurka ta yi mursisi a kan azabtar da Musulman Falastina da ake yi. BBC ta ce Isra’ila tana cigaba da kai wa yankin Gaza hari har gobe.

Kafin yanzu an ji Saudiyya da Masar sun bukaci a dakata da luguden wuta bayan Isra'ila ta harba wani makamin da ya yi kaca-kaca da gidan jagoran kungiyar Hamas.

Kawo yanzu babu tabbacin adadin mutanen da aka kashe ko suka ji rauni a hare-haren da aka shafe kwanaki fiye da bakwai ana yi tsakanin Isra’ila da 'Yan Hamas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel