Yanzu-yanzu: Isra'ila ta rusa ofishin gidan jaridar Aljazeera dake Gaza, Falasdin

Yanzu-yanzu: Isra'ila ta rusa ofishin gidan jaridar Aljazeera dake Gaza, Falasdin

- Kwanaki biyar a jere, ana rikici tsakanin Falasdinu da Isra'ila

- Isra'ila na cigaba da rusa gidaje da ofishoshin mutanen Falasdinu

- Abin yanzu ya shafi ofishohin gidajen jaridar AlJazeera da AP

Kasar Isra'ila ta kai hari gidan benen da ofishin gidan jaridar AlJazeera, AP da wasu kamfanonin jaridar ke ciki a birnin Gaza, kasar Falasdin.

A bidiyon da Alarabiya ta dauka, an ga yadda makami mai linzami da Isra'ila ta harba ya rusa ginin har kasa.

Mai ginin benen, Jawwad Mahdi, ya bayyana cewa hukumar Sojin Isra'ila ta kirashi cewa za'a kaiwa gidansa hari.

Ya bayyana cewa an fada masa ya sanar da wadanda ke cikin ginin su tattara inasu-inasu su bari cikin awa guda.

KU KARANTA: Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari

Kalli bidiyon:

DUBA NAN: Rikici da Falasdinawa: Kamfanonin jirage sama 7 sun dakatad da zuwa Isra'ila

A bangare guda, akalla Falasdinawa 139 ne suka rasa rayukansu - ciki akwai kananan yara 40 - a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa kuma kimanin mutum 1000 sun jigata suna jinya.

Isra'ila ta cigaba da ruwan rokoki kan yankin Gaza kuma ta fara tura Sojojin kasa da motocin yaki cikin Falasdin.

A Arewacin Gaza, Bier Hanoun da Jabalya, na cikin wuraren da Isra'ila ke cigaba da budewa wuta.

Hakazalika a gabashin Gaza inda aka yi ruwan bama-bamai a Shuna'iah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel