Ba zamu je Abuja sulhu da NLC ko FG ba idan ba'a dawo da lantarki ba, El-Rufa'i

Ba zamu je Abuja sulhu da NLC ko FG ba idan ba'a dawo da lantarki ba, El-Rufa'i

- Da alamun gwamnan jihar Kaduna zai tafi zaman sulhun da gwamnatin tarayya ta shirya

- FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu

- Amma gwamnan ya bada sharadi guda daya da za'a cika

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya bayyana cewa har yanzu bai ga hujjan cewa yan kungiyar kwadago sun janye daga yajin aiki kamar yadda sukayi ikirari ba.

A cewarsa, rashin dawo da wutan lantarki wanda abune mai muhimmanci ya nuna cewa ba da gaske suke ba.

Ya jaddada cewa ba za'a yi sulhu ba muddin ba'a dawo da lantarki ga al'ummar jihar Kaduna ba.

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita da yammacin Laraba.

Yace: "Gwamnatin jihar Kaduna har yanzu ba ta ga hujjan cewa NLC ta janye daga fito-na-fito da tattalin arzikin jihar ba. Har yanzu jama'armu ba su da wutan lantarki tun bayan da aka kashe ranar 16 ga Mayu, 2021."

"Gwamnatin jihar na jaddada cewa wajibi ne a dawo da lantarki. Idan ba haka ba, babu wani zaman sulhu."

"Babu jami'in gwamnatin jihar da zai je Abuja zaman da FG ko NLC muddin ba'a dawo da lantarki ba."

"Kuma muna daura alhaki kan gwamnatin tarayya kan gazawarta wajen nuna iko kan kamfanin TCN. Babu wuta, babu zama."

KU DUBA: Nan da 2022 sabon kamfanin jirgin Nigeria Air zai fara aiki, Hadi Sirika

DUBA NAN: FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu

NLC ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki 5 a Kaduna, Shugaban NLC, Ayuba Wabba ya sanar da shawarar, ya ce ya yi hakan ne don girmama gayyatar da FG ta yi don sasanta rikicin da ke tsakanin kungiyar kwadagon da gwamnatin jihar Kaduna, in ji TVC.

Channels Tv ta ruwaito cewa, a safiyar yau, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige ya shiga cikin takun-saka tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyoyin kwadago ta hanyar gayyatar bangarorin biyu zuwa taron sasantawa.

Ngige ya umarci bangarorin biyu da su ci gaba da kasancewa a yadda suke har zuwa lokacin da za a sasanta batutuwan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel