Da duminsa: Nan da 2022 sabon kamfanin jirgin Nigeria Air zai fara aiki, Hadi Sirika

Da duminsa: Nan da 2022 sabon kamfanin jirgin Nigeria Air zai fara aiki, Hadi Sirika

- Bayan shekara-shekaru, za'a dawo da kamfanin sufurin jirgin sama mallakin gwamnati

- Minista Siriki yace gwamnati zata dankawa masu hannun jari gudanar da kamfanin

- Ya bayyana cewa annobar Korona ta jinkirta kaddamar da kamfanin shekarar nan

Ministan Sufurin jirgin sama, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana cewa sabon kamfanin jirgin sama mallakin gwamnatin tarayya, Nigeria Air zai fara aiki a farkon shekarar 2022.

Sirika ya bayyana hakan ne yayinda hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartaswar a Abuja, rahoton TheCable.

Ya ce an dade da shirin samar da wannan kamfani na kasa kuma zai fara aiki a farkon 2022, da farashi mai sauki fiye da kamfanoni masu zaman kansu.

Sirika ya ce wannan sabon kamfanin jirgin zai taimakawa yan Najeriya wajen samar da aikin yi ga miliyoyin mutane.

Ya ce annobar COVID-19 ce ta sabbaba dage shirin kaddamar da kamfanin zuwa karshen 2021.

KU KARANTA: NLC Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Tsunduma a Kaduna

Da duminsa: Nan da 2022 sabon kamfanin jirgin Nigeria Air zai fara aiki, Hadi Sirika
Da duminsa: Nan da 2022 sabon kamfanin jirgin Nigeria Air zai fara aiki, Hadi Sirika
Asali: UGC

DUBA NAN: Ba zamu je Abuja sulhu da NLC ko FG ba idan ba'a dawo da lantarki ba, El-Rufa'i

A bangare guda, Gimba Kumo, tsohon sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai taba samun gayyata daga hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ba kafin ta ce tana nemansa a kan badakalar kudi har $65 miliyan yayin da yake manajan daraktan bankin gidaje na tarayya.

Kumo ya sanar da hakan a wata wasika da ya rubuta zuwa shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye mai kwanan wata 18 ga Mayun 2021.

A ranar Alhamis da ta gabata ne hukumar ICPC tace tana neman Kumo ruwa a jallo tare da Tarry Rufus da Bola Ogunsola a kan wata damfara da ake zarginsu da ita, jaridar The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng