Ko kana so, ko ba ka so, muna so ka yi mana takara – Magoya baya sun fadawa Osinbajo

Ko kana so, ko ba ka so, muna so ka yi mana takara – Magoya baya sun fadawa Osinbajo

- Osinbajo Grassroots Organisation ta na tare da Yemi Osinbajo har gobe

- Kungiyar ta ce ko Osinbajo bai sha’awar takara a 2023, ta na bayan shi

- Shugaban Osinbajo Grassroots Organisation ya ce Osinbajo ne gwaninsu

Kungiyar Osinbajo Grassroots Organisation ta dage a kan ya kamata a ba Farfesa Yemi Osinbajo tikitin takarar shugaban kasa a APC a zabe mai zuwa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan kungiya ta ‘yan siyasa tana da burin ganin mataimakin shugaban Najeriyar ya samu tutar tsayawa takara a 2023.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan mataimaki shugaban kasar ya tabbatar da cewa bai nuna sha’awar neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023 ba.

KU KARANTA: Mataimakin Shugaban Ƙasa Osinbajo ya yi magana a kan zaben 2023

Shugaban kungiyar Osinbajo Grassroots Organisation, Folusho Ojo ‘Fosh’, yace ko Yemi Osinbajo ya na so, ko bai so, suna goyon bayan shi a babban zaben 2023.

Folusho Ojo ya dage, ya ce: “Kungiyar OGO ta na kan batunta na cewa Osinbajo yana da duk abin da ake bukata domin a kai kasar nan zuwa tudun mun-tsira.”

“Bai aike mu domin muyi masa wannan aiki ba. Bai daura mana nauyin yi masa yakin neman zabe ba. Mu matasa ne da mata wadanda mu ka yarda da shi.”

Kungiyar magoya bayan ta ce za ta tallata dabi’un Yemi Osinbajo da su ka sa ta ke sha’awarsa. Jaridar Vanguard ta fitar da irin wannan rahoto a ranar Talata.

KU KARANTA: Burina in yi aiki ba neman Shugaban kasa ba - Osinbajo

Ko kana so, ko ba ka so, muna so ka yi mana takara – Magoya baya sun fadawa Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: @ProfOsinbajo
Asali: Twitter

“Shi ne wanda muka yarda da shi. Saboda haka, ba tare da la’akari da matsayarsa ba, za mu cigaba da tallata shi, mu rika fadawa Duniya halayensa na kwarai.”

“Ganin yadda ya samu karbuwa da shahara, muna kiran mutanenmu a fadin kasar nan, su yi ta yada manufofin da aka san mataimakin shugaban kasar da su.”

Ya ce: “Osinbajo ne wanda mu ka yarda da shi, kuma za mu cigaba da mara masa baya a yau ko a gobe, ko yana neman mulki ko ba ya nema, ko da ya bar kujera.”

Dazu kun ji cewa bayan an kai korafin cin kudin saida fam din takara, jami’an hukumar EFCC sun soma binciken wasu daga cikin manyan jam’iyyar PDP na kasa.

A yau za a tasa Sakataren gudanarwa, da mai binciken kudi da kuma darektan kudin PDP a ofishin EFCC, inda za su amsa tambayoyi kan zargin da ake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel