Gwamnatin tarayya ta sa baki cikin rikicin El-Rufa'i da NLC

Gwamnatin tarayya ta sa baki cikin rikicin El-Rufa'i da NLC

- FG ta bayyana cewa bata jahilci abinda ke faruwa a jihar Kaduna ba

- Yan kungiyar ma'aikatun man fetur NUPENG sun yi barazanar shiga yajin idan ba'a bi a hankali ba

- An shiga kwana na uku a yajin aikin kwanaki biyar da NLC ta sanar

Gwamnatin tarayya ranar Talata ta sa baki cikin rashin jituwan dake gudana tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyoyin kwadagon Najeriya.

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC da TUC sun shiga yajin aiki ne na kwanaki biyar da kuma zanga-zanga kan sallamar ma'aikata 7,000 da gwamnati tayi.

Amma, gwamnatin jihar ta jaddada cewa ba zata iya cigaba da biyan ma'aikatan shi yasa ta koresu.

Ministan Kwadago, Chris Ngige, a jawabin da yayi ya yi kira ga bangarori biyu su yi sulhu da juna.

Mataimakin diraktan labarai a ma'aikatar kwadago ya saki jawabin ga manema labarai.

KU KARANTA: Kada ku nuna imani wajen ragargazan yan kungiyar IPOB, Sifeto Janar ga Yan sanda

Gwamnatin tarayya ta sa baki cikin rikicin El-Rufa'i da NLC
Gwamnatin tarayya ta sa baki cikin rikicin El-Rufa'i da NLC Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda biyu

"Mun san abinda ke faruwa a jihar Kaduna. Matsalar kwadago ne kuma zama yajin aiki," Ngige yace.

"Muna rokon gwamnan Kaduna kada ya ja lamarin inda ba za'a iya shawo kanta ba. Hakazalika muna kira ga shugabannin kwadago su tsagaita wuta domin samun daman yin sulhu."

"Ma'aikatata na shiga lamarin yanzu kuma tana kira ga bangarorin biyu su baiwa sulhu dama."

Ma'aikatar ta yi kira ga dukkan ma'aikata masu muhimmanci irinsu Likitoci da ma'aikatan jinya kada su shiga yajin aikin.

A bangare guda, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce wadanda suka katse kasuwanci a jihar da sunan yajin aiki zasu dandana kudarsu.

A cikin kwanakin da suka gabata, mambobin kungiyar kwadago ta kasa da El-Rufai sun yi artabu a kan hukuncin gwamnatin jihar na sallamar sama da ma'aikata 4,000 a jihar.

A sakamakon hakan, kungiyar kwadago karkashin shugabancin Ayuba Wabba ta shiga yaji aikin kwanaki biyar wanda ta fara a ranar Litinin, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel