Duniya juyi-juyi: Jawabin Nasir El-Rufai a wajen zanga-zangar da aka yi wa Goodluck Jonathan

Duniya juyi-juyi: Jawabin Nasir El-Rufai a wajen zanga-zangar da aka yi wa Goodluck Jonathan

- Nasir El-Rufai da wasu sun yi wa Gwamnatin PDP zanga-zanga a 2012

- Gwamnan ya soki karin kudin man fetur da Goodluck Jonathan ya yi

- A yau, Gwamnan na Kaduna ya na yaki da masu yi masa zanga-zanga

A lokacin da gwamnatin Goodluck Jonathan take mulki tsakanin Mayun 2010 zuwa Mayun 2015, Nasir El-Rufai ya na cikin manyan ‘yan adawarta.

Malam Nasir El-Rufai da wasu ‘yan adawa a lokacin, sun jagoranci zanga-zangar OccupyNaija sa’ilin da gwamnatin tarayya ta kara kudin man fetur.

Nasir El-Rufai wanda ya zama gwamna a 2015 sune ‘yan gaba-gaba, tare da tsohon Sanata Dino Melaye da tsohon Ministan tarayya, Femi Fani-Kayode.

KU KARANTA: Giyar mulki ke dibar El-Rufai, za mu rufe kasar nan - NUPENG

A wajen zanga-zangar, za a ji Sanata Dino Melaye ya na cewa:

“Zan mika abin magana zuwa ga Malam Nasir El-Rufai, bayan jawabinsa, za mu saurari Femi Fani-Kayode, daga nan sai mu wuce kasuwar Wuse.”

Sai aka yi shewa!

Da tsohon Ministan birnin tarayyar ya karbi abin magana, sai ya soki gwamnati mai-ci a lokacin, ya nuna ya kamata a rika saida litar man fetur a kan N40 rak:

“Mutanen Najeriya masu daraja! Ina so in yaba wa kokarinku na tsaya wa tsayin-daka.”

“Za mu cigaba da yakar wannan gwamnati, har sai tayi abin da ya kamata.

Duniya juyi-juyi: Jawabin Nasir El-Rufai a wajen zanga-zangar da aka yi wa Goodluck Jonathan
Gwamna Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

KU KARANTA: Femi Fani-Kayode ya sauya sheka jam'iyyar APC - Bello

“Abin da ya dace shi ne, gwamnati ta rage kudin da suke kashewa, a tabbatar da matatunmu sun dawo aiki.”

“Domin mu saye man fetur, ba ma a kan N65 ba, a kan N40!”

“Yanzu za mu wuce zuwa kasuwar Wuse, sai mu zarce filin taron ‘Eagle square’”

Daga nan kuma Femi Fani-Kayode ya karbi abin magana, ya yi kaca-kaca da gwamnatin PDP. Amma daga baya, Fani-Kayode ya bar APC, ya koma PDP.

A kwanakin baya ne kuma aka ji Yahaya Bello ya fito ya na cewa Femi Fani-Kayode zai dawo APC, duk da irin sukar da ya rika yi wa gwamnatin Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel