‘Yan siyasar Kudu sun fito da mutum 11 da za su nemi takarar Shugaban jam’iyyar PDP
- Masu harin kujerar Shugaban jam’iyyar PDP na kasa a 2021 sun fara shiri
- Akwai ‘Yan takara akalla 11 da su ka fito daga yankin Kudu maso yamma
- Tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Peter Fayose yana cikin masu neman kujerar
Wata kungiya ta magoya bayan PDP a kudu maso yammacin Najeriya, Alliance for PDP South-West, sun fito da masu neman kujerar shugaban jam’iyya.
Alliance for PDP South-West ta kawo jerin ‘yan takara 11 daga Kudu maso yammacin kasar nan.
Daga cikin wadanda aka fito da sunayensu akwai: tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose.
KU KARANTA: Mata suna so Gwamna Bello ya nemi shugaban kasa a 2021
Haka zalika jerin da aka fitar ya na dauke da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa (yankin Kudu), Olabode George da tsohon jigon PDP, Injiniya Segun Oni.
Tsohon ‘dan takarar gwamnan Legas, Jimi Agbaje, tsohon sakataren jam’iyyar PDP, Farfesa Wale Oladipo, da kuma Dr. Charles Akitoye suna cikin ‘yan takarar.
Ragowar ‘yan takarar sune: Jide Adeniji; Olusola Ebiseni; Sanata Bode Olajumoke. Sai kuma tsohon ‘dan takarar gwamnan jihar Ondo, Eyitayo Jegede SAN.
Masu takarar za su nemi kujerar Prince Uche Secondus, wanda wa’adinsa zai kare a karshen 2021. Amma ana rade-radin cewa shugaban jam’iyyar zai nemi tazarce.
KU KARANTA: ‘Yan Majalisar Dattawa su na so su sauke Ahmad Lawan
Punch ta rahoto Segun Oni ya na cewa suna tare ne da tsohon gwamna, Prince Olagunsoye Oyinlola. Oni ya ce har yanzu Oyinlola bai tsaida magana ba.
Idan za a tuna, Farfesa Wale Oladipo ya taba neman kujerar shugaban jam’iyyar PDP na kasa a 2017.
Watakila tsohon gwamna Ayo Fayose wanda yake samun sabani da gwamnan Oyo, Seyi Makinde, zai jarraba sa’arsa a zaben da za a gudanar a karshen badi.
Bayan an soma jin jita-jia, an ji cewa shugaban rikon kwaryan APC, Mai Mala Buni yace ba su kintsa ba, da wahala a gudanar da zaben shugabanni a Yuni.
Jam’iyyar APC ta musanya rade-radin cewa an sa lokacin da za a yi zabukan ta na kasa. Sanata John James Akpanudoedehe ya bada wannan sanarwa ne a jiya.
Asali: Legit.ng