El-Rufa'i yace masu zanga-zanga tamkar yan bindiga ne, ya sallami Malaman jami'ar KASU da suka shiga

El-Rufa'i yace masu zanga-zanga tamkar yan bindiga ne, ya sallami Malaman jami'ar KASU da suka shiga

- Gwamna Nasir El-Rufai ya sha alwashin sallamar dukkan ma'aikatan da suka shiga zanga-zangar kungiyar kwadago a jihar

- An kulle gidajen mai, bankuna, tashohiin jirgin sama da kasa, dss

- El-Rufa'i ya sallami malaman jinya, malaman jami'a da suka shiga yajin aikin

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya siffanta shugabannin kungiyar kwadago, NLC, da suka shirya yajin aiki da zanga-zanga kan sallamar ma'aikata a jihar matsayin yan bindiga.

Ya lashi takobin hukuntasu, inda ya tuhumcesu da lalata dukiyoyin gwamnati da kuma tayar da tarzoma.

A cewar El-Rufa'i, basu da banbanci da yan bindiga masu garkuwa da mutane da suka addabi al'ummar jihar.

Hakazalika ya bada umurnin sallamar Malamn jami'ar Kaduna KASU da suka shiga yajin aikin na kwanaki 5.

Mai magana da yawun El-Rufa'i, Muyiwa Adekeye, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Litinin a Tuwita.

Yace: "Gwamnatin Kaduna na ganin wannan abin da NLC keyi tamkar yan bindiga masu garkuwa da mutane da suka addabi al'umma."

"Yan bindiga na amfani da makamai, amma NLC na amfani da nasu wanda manufarsu guda: hana mutane yanci, dakile tattalin arziki, da kuma lalata dukiyoyin al'ummar Kaduna."

KU KARANTA: El-Rufai ya sha alwashin koran ma'aikatan da suka yi zanga-zanga da NLC

El-Rufa'i yace masu zanga-zanga tamkar yan bindiga ne, ya sallami Malaman jami'ar KASU da suka shiga
El-Rufa'i yace masu zanga-zanga tamkar yan bindiga ne, ya sallami Malaman jami'ar KASU da suka shiga Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

DUBA NAN: Yajin aikin Kaduna: Ka sasanta da kungiyar kwadago, gwamnonin APC sun shawarci El-Rufai

Kungiyar kwadago Najeriya NLC a ranar Litinin ta kaddamar da yajin aiki kare dangi na kwanaki 5 a jihar Kaduna kan yunkurin da gwamnatin jihar keyi na korar dubban ma'aikata.

Yan kwadagon sun gudanar da zanga-zanga inda suka lashi takobin durkusar da jihar har sai gwamnatin jihar ta amsa bukatunsu.

Sakamakon haka an rufe ma'aikatun gwamnati, bankuna, tashohon jirgin sama da na kasa, gidajen mai, da kuma kamfanonin wutan lantarki.

Shi kuma gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i, ya lashi takobin cewa ba zai sauraresu ba.

A ranar Asabar El-Rufai yace gwamnatinsa ba za ta saurari kowanne irin bacin suna ba, tare da jaddada cewa ba zai yuwu ya kashe kashi 84 zuwa 96 na kudin da yake samu daga gwamnatin tarayya ba zuwa biyan albashi.

Gwamnatin jihar tace ana ta gangamin shirya mata karairayi da ikirari marasa tushe inda aka ce ta sallama ma'aikata 4000 kuma ta daina biyan sabon mafi karancin albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng