Kafin ya cika shekaru 2 a ofis, Sanatoci sun fara kutun-kutun, a tunbuke Shugaban Majalisa

Kafin ya cika shekaru 2 a ofis, Sanatoci sun fara kutun-kutun, a tunbuke Shugaban Majalisa

- Hon. Sergius Ogun yace an fara shirin sauke Ahmad Lawan a Majalisar Dattawa

- Sukar taron da gwamnonin Kudu su ka yi ya jawowa Dr. Ahmad Lawan matsala

- Ogun yace suna ganin Lawan alakakai ne wajen yi wa fasalin kasa garambawul

A wani yunkurin kawo sauyi a majalisar dattawa, Sanataoci sun fara maganar sauke shugaban majalisa, Dr. Ahmad Ibrahim Lawan, daga kujerarsa.

Jaridar This Day ta samu labari a ranar Litinin, 17 ga watan Mayu, 2021, cewa ana kokarin tsige Ahmad Ibrahim Lawan daga mukamin da yake a kai.

‘Dan majalisa mai wakiltar shiyyoyin Esan a majalisar wakilai, Hon. Sergius Ogun, ya tabbatar da wannan a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabiji.

KU KARANTA: CAN ta maida martani kan shawarar da Babangida ya bada

Rahotanni sun tabbatar da cewa Honarabul Sergius Ogun, ya bayyana cewa akwai shirin da ake yi yanzu haka a kasa, na tunbuke Sanata Ahmad Lawan.

A cewar ‘dan majalisar, Lawan zai iya rasa kujerarsa a makon nan. Hakan na zuwa ne bayan ya soki taron da gwamnonin jihohin Kudu su ka yi a Asaba.

“Muna kokarin yi wa kundin tsarin mulki garambuwal, shugaban majalisar tarayya (Ahmad Lawan), ya na neman hana mu, hakan ba za ta yiwu ba."

“Yana sukar gwamnoin Kudu saboda sun ce a sake wa Najeriya fasali. Bai yadda da yunkurin nan ba, meyasa zai rika magana haka?" Inji Hon. Sergius Ogun.

KU KARANTA: Gwamnonin PDP suna so a karawa Jihohi karfi

Kafin ya cika shekaru 2 a ofis, Sanatoci sun fara kutun-kutun, a tunbuke Shugaban Majalisa
Sanata Ahmad Lawan OON Hoto; www.tribuneonlineng.com
Asali: Facebook

“Ya fito ya na wannan kalamai ya nuna bai dace ya zama shugaban majalisar dattawa ba, kuma Sanatocin kudu za su yi wani abu a kan shi a makon nan.”

“Muna maganar sauke shi ne? Wanene shugaba? Shugaban majalisar tarayya? Idan za a yi maganar tsige shugaban kasa, wa zai jagoranci batun? Shi!”

Ogun yake cewa ya tabbata ‘yan majalisa sun soma shirin yadda za a sauke Lawan daga kujerarsa, amma bai da tabbacin akwai adadin da ake bukata.

A safiyar yau kun ji cewa ana cigaba da zuga ‘Yan Majalisar wakilai da Sanatoci su dauki mataki idan ba ta canza zani ba, su tunbuke shugaban kasar Najeriya.

Wani lauya ya yi kira ga ‘Yan Majalisa su tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda matsalar rashin tsaro, ganin yadda lamarin ya ki cinyewa har yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel