Yajin aiki: Kuyi hakuri ku dagawa El-Rufa'i kafa, Kungiyar Gwamnoni ta roki NLC

Yajin aiki: Kuyi hakuri ku dagawa El-Rufa'i kafa, Kungiyar Gwamnoni ta roki NLC

- Gwamnan Kaduna ya yi fito-na-fito da yan kungiyar kwadago a jiharsa

- An shiga yajin aikin kwanaki biyar fari daga ranar Litnin, 17 ga Mayu, 2021

- An kulle gidajen mai, bankuna, tashohiin jirgin sama da kasa, dss

Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF a ranar Litinin ta mika kokon baranta ga kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta tayi hakuri ta tattauna da gwamnatin jihar Kaduna.

Shugaban kungiyar, Dr Kayode Fayemi, wanda shine gwamnan jihar Ekiti ya bada hakurin ne a jawabin da ya saki a madadin takwarorinsa a birnin tarayya Abuja.

Fayemi yace babu cigaban da za'a samu idan aka cigaba da rikici da juna kan wannan lamari.

Hakazalika ya shawarci yan kwadagon cewa idan abin nasu ya wuce gona da iri zai zama illa ga su kansu ma'aikatan.

Wani sashen jawabin yace, "Kungiyar NGF na kira ga yan kwadago su duba su gani babu wani nasara da aka taba samu daga rikici da tayar da hankali."

"Hakazalika NGF na tunawa NLC cewa wannan abu da takeyi na iya zama illa ga mambobinta saboda irin wahalan da aka sha a shekarar 2020."

KU DUBA: El-Rufa'i ya alanta neman shugaban NLC, Ayuba Waba, ruwa a jallo

Yajin aiki: Kuyi hakuri ku dagawa El-Rufa'i kafa, Kungiyar Gwamnoni ta roki NLC
Yajin aiki: Kuyi hakuri ku dagawa El-Rufa'i kafa, Kungiyar Gwamnoni ta roki NLC
Asali: Twitter

Ya cigaba da cewa: "Saboda haka NGF ta shawarta NLC ta yi amfani da daman tattaunawa da gwamnatin jihar Kaduna ta bada domin shawo kan lamarin."

"Kada a kalli wannan abu a matsayin cin fuska ko kokarin sallaman ma'aikata haka kawai. A iya saninmu dukkan jihohi na fama da matsaloli kuma mafita ita ce kowace jiha ta samawa kanta yadda zata magance matsalolin ba tare da take hakkin mutane ba."

KU KARANTA: A shekara 6, sai da Gwamna El-Rufai ya sallami ma’aikata 60,000 daga aiki – Falana, ASCAB

Kungiyar kwadago Najeriya NLC a ranar Litinin ta kaddamar da yajin aiki kare dangi na kwanaki 5 a jihar Kaduna kan yunkurin da gwamnatin jihar keyi na korar dubban ma'aikata.

Yan kwadagon sun gudanar da zanga-zanga inda suka lashi takobin durkusar da jihar har sai gwamnatin jihar ta amsa bukatunsu.

Sakamakon haka an rufe ma'aikatun gwamnati, bankuna, tashohon jirgin sama da na kasa, gidajen mai, da kuma kamfanonin wutan lantarki.

Shi kuma gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i, ya lashi takobin cewa ba zai sauraresu ba.

A ranar Asabar El-Rufai yace gwamnatinsa ba za ta saurari kowanne irin bacin suna ba, tare da jaddada cewa ba zai yuwu ya kashe kashi 84 zuwa 96 na kudin da yake samu daga gwamnatin tarayya ba zuwa biyan albashi.

Gwamnatin jihar tace ana ta gangamin shirya mata karairayi da ikirari marasa tushe inda aka ce ta sallama ma'aikata 4000 kuma ta daina biyan sabon mafi karancin albashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel