2023: Duka Gwamonin PDP za su yi zama na musamman a kan yadda za su tunkari APC

2023: Duka Gwamonin PDP za su yi zama na musamman a kan yadda za su tunkari APC

- Gwamnonin jam’iyyar PDP za su yi taro a garin Ibadan a farkon makon nan

- Jam’iyyar PDP za ta tattauna a kan abin da ya shafi sha’anin tsaro da tattali

- Ana sa ran duka Gwamnonin PDP 15 za su halarci wannan zaman da za ayi

Gwamnonin da ke karkashin jam’iyyar PDP za su yi zama a ranar Litinin, 17 ga watan Mayu, 2021, su tattauna kan abin da ya shafi Najeriya.

Jaridar The Cable ta ce babbar jam’iyyar hamayyar kasar ta bada sanarwar wannan taro da za ayi ne a wani jawabi da ta fitar a ranar Lahadi da yamma.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana mana, gwamnonin za su yi zaman ne a garin Ibadan, jihar Oyo.

KU KARANTA: "Babu tabbacin APC za ta iya kai labari ba tare da Tinubu ba"

Darekta-Janar na kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP na kasa, Cyril Maduabum, ya ce za a yi taron yau ne domin a tsara dabarun yakin neman zabe.

Cyril Maduabum yake cewa za su fito da tsare-tsaren da za su ba ‘yan Najeriya madadin gwamnatin APC da ta shafe shekaru kusan shida a mulki.

Maduabum ya ce gwamnoni 15 za su samu halartar wannan taro a karkashin shugaban kungiyar gwamnonin PDP, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal.

Mai girma Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal da sauran abokan aikinsa, sun fara shirya wa yadda za su karbe mulkin kasa daga hannun jam’iyyar APC a 2023.

KU KARANTA: Jigon PDP ya soki salon Gwamnatin Buhari

2023: Duka Gwamonin PDP za su yi zama na musamman a kan yadda za su tunkari APC
Wasu Gwamonin PDP
Asali: Twitter

“Taron zai kuma duba halin da kasa ta ke ciki, musamman bangaren tattalin arziki da tsaro.

“Sannan za a tsara dabarunn da za su taimaka wa PDP, wajen fito da ita a matsayin madadin gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki.” Inji Cyril Maduabum.

Wannan shi ne zai zama taro na biyu da gwamnonin jam’iyyar PDP su ka yi a ‘yan kwanakin nan. A farkon watan Afrilu, an yi irin wannan zama a jihar Benuwai.

Kun ji cewa wasu Matasan Najeriya sun ce babu wanda zai iya gyara Najeriya idan ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba, sun soma yi masa kamfe.

Wata kungiyar matasa ta bayyana kudirinta na sayawa tsohon shugaba Goodluck Jonathan fam din shiga takara, kuma ta dauki nauyin yakin neman zabensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel