Abin da zai faru muddin APC ta hana Tinubu takarar Shugaban kasa – Tsohon ‘Dan Majalisa

Abin da zai faru muddin APC ta hana Tinubu takarar Shugaban kasa – Tsohon ‘Dan Majalisa

- Saheed Akinade-Fijabi ya na ganin babu wanda zai iya cewa komai a kan 2023

- Hon. Fijabi ya ce wata jam’iyya za ta bullo idan aka hana Bola Tinubu tutar APC

- Tsohon ‘dan majalisar ya bayyana cewa mutanen Najeriya ba su da tabbas a siyasa

A karshen makon nan ne, tsohon ‘dan majalisar tarayya, Saheed Akinade-Fijabi, ya tabo batun wanda za a ba takara a jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

Honarabul Saheed Akinade-Fijabi ya bayyana cewa za a samu bayyanar wata jam’iyya dabam, idan APC ba ta ba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tikiti ba.

Saheed Akinade-Fijabi wanda ya taba wakiltar yankin jihar Oyo a majalisar tarayya, yana ganin za a iya samun matsala idan Jigon APC bai samu takara ba.

KU KARANTA: Ban yi amfani da kujerar mulki wajen zalunci ba - Jonathan

A ganin Akinade-Fijabi, wata jam’iyya ta dabam za ta bullo, ta doke APC da PDP mai adawa, idan APC ba ta tsaida tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu ba.

Tsohon ‘dan majalisar ya na ganin wannan jam’iyya da za ta fito, za ta taimaka wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wajen ganin burinsa na yin mulki, ya tabbata.

Punch ta ce Fijabi ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi hira da shi a wani gidan rediyo a Ibadan.

An yi wa Fijabi tambaya ne game da burin Bola Tinubu na zama shugaban kasa da takarar 2023, inda ya bayyana cewa komai na iya faru wa a zaben mai zuwa.

KU KARANTA: Matasa suna yi wa Jonathan dawo-dawo a 2023

Abin da zai faru muddin APC ta hana Tinubu takarar Shugaban kasa – Tsohon ‘Dan Majalisa
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

‘Dan siyasar ya na ganin ba za a iya cewa komai a kan yadda zaben zai kasance ba, sai abin da aka gani. Fijabi yake cewa mutanen Najeriya ba su da wani tabbas.

“Ba a gane gaban mutanenmu, akwai yiwuwar wata jam’iyya ta bullo, ta doke sauran jam’iyyun da ake da su (PDP da APC) idan aka hana Bola Tinubu tuta a 2023.”

Amma a jihar Oyo, Akinade-Fijabi ya na ganin APC za ta dawo da karfinta a zabe mai zuwa, saboda yunkurin sulhunta ‘ya ‘yan jam’iyyar da ake ta kokarin yi.

A jiya ne aka ji tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya ba gwamnatin tarayya shawara kan yadda za a magance matsalar rashin tsaro.

Babangida yace yana da yaƙinin cewa matukar gwamnati ta amince ta sake zama domin yin sabon tunani kan rashin tsaro a ƙasar nan, to zata cimma nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng