Da Najeriya kasar da aka cigaba ce, da tuni an fatattaki Shugaba Buhari - Ayo Adebanjo
- Shugabann Afenifere ya soki Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari
- Ayo Adebanjo ya ce hakurin mutane ya sa har gobe Buhari yake mulki
- Dattijon ya na ganin matasan da su ke zamani yanzu sun jama’a kunya
Shugaban kungiyar Afenifere, Ayo Adebanjo, ya ce ba don mutanen kasar nan suna da yawan hakuri ba, da Muhammadu Buhari ya bar ofis tun tuni.
Da jaridar This Day ta yi hira da Ayo Adebanjo a ranar Talata wajen bikin cikan Cif Reuben Fasoranti shekara 95 da haihuwa ne, ta yi wannan bayani.
Ayo Adebanjo yake cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ba mutanen kasar nan kunya.
KU KARANTA: 'Yan fashi sun fada hannun 'Yan Sanda
“Na fada masu cewa da a wata kasa da aka cigaba ne, da tuni an yi waje da shi. Da ya san mutuncin kansa, da ya yi gaba, domin abubuwa sun jagwalgwale.”
“Shugabancin me yake yi? Sha’anin rashin gaskiya, tsaro, ko ilmi? Dokar kasa ta daina aiki shekaru uku da suka wuce.” Inji shugaban Afenifere.
“Saboda ‘yan Najeriya suna da yawan hakuri ne kurum, shiyasa yake cigaba da zama a ofis.”
Jagoran kungiyar Yarbawan ya ce matasa sun bada kunya, ya ce ya kamata su ji kunyar kansu. “Masu taso wa sun ba kasar nan kunya. Ba haka abubuwa suka cabe a lokacin da mu ke neman ‘yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka ba.”
KU KARANTA: Mutane su kara hakuri - Buhari
"Suna so tsofaffi suyi masu yakinsu. Me zai sa mutane irina a 93 da Baba Fasoranti yana 95 su cigaba da gwagwarmaya. Ina wadanda suke ‘Yan 30 da 40?”
“Lokacin da mu ke shekarunsu, mu na kan tituna a Legas, Landan, ko ina.”
A karshe ya ce: “Da safe ka na PDP, da rana ka na APC, da yamma ka na SDP, kuma sai su ce su matasa ne, ya kamata matasa su ji kunyar kansu.”
A yau ne aka ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi karamar sallah a fadarsa dake Aso Rock Abuja.
Kamar yadda hotunan da hadiminsa, Buhari Sallau ya wallafa a shafinsa na Twitter suka nuna, shugaban kasan ya sallaci idin karamar sallah tare da iyalansa.
Asali: Legit.ng