‘Yan bindiga sun addabe mu, mun yi asarar dukiyar sama da N300m inji mutanen Fulani

‘Yan bindiga sun addabe mu, mun yi asarar dukiyar sama da N300m inji mutanen Fulani

Wasu al’ummar Fulani a Kwara sun yi kira ga gwamnati ta binciki hare-haren da wasu tsagerun matasa su ke yawan kai masu a ‘yan kwanakin nan.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutanen yankin suna kukan cewa su ma sun shiga tarkon miyagun ‘yan bindigan da suke garkuwa da mutane.

Mai magana da yawun bakin al’ummar Fulani a Kwara, Alifa Dan-Fulani Modibbo, ya ce su kansu ba su kubuta daga hannun wadannan ‘yan bindiga ba.

KU KARANTA: Sarki ya ce Talakawansa su yi fito da fito da 'Yan bindiga

Alhaji Alifa Dan-Fulani Modibbo yake cewa sun yi asarar dukiyoyi da-dama a sanadiyyar hare-haren da wasu matasa suka rika kai wa mutanen Fulani.

Kakakin Fulanin yake cewa sun rasa dukiyar kusan Naira miliyan 300, daga ciki har da motoci, shanu da da tumaki 2,000, gidaje 50, da otel da sauransu.

Alifa Dan-Fulani Modibbo ya karyata rade-radin da ake yi na cewa an kona otel din Alhaji Ramoni ne saboda ya na da alaka da masu garkuwa da mutane.

“A ranar 27 ga watan Afrilu, wasu sojoji sun duro yankin Fulani a Odo Owa, suna neman masu garkuwa da mutane, aka fada masu cewa Fulanin nan sun dade a nan, sun shafe sama da shekaru 100 suna zaune a wannan yanki.” Inji Modibbo.

‘Yan bindiga sun addabe mu, mun yi asarar dukiyar sama da N300m inji mutanen Fulani
Sufetan 'Yan Sandan Najeriya
Asali: Facebook

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kona ofishin 'Yan Sanda

“Daga baya, jami’an tsaro suka dawo, suna binciken makamai da ake zargin an boye a nan, amma ba a samu komai. Kadin mu sani, sai ga matasa sun duro mana”

“Dandazon matasa suka shiho, suka kona mana dukiya, suka sace mana kudi a gaban jami’an tsaro. Suka dauke Ramon, suka ce hakan zai hana a kai masu hari.”

Fulanin sun wanke Ramon, suka ce kasuwancin dabbobi yake yi a Omu Aran da Odo Owa, sai otel a Omu Aran, suka ce an shiga gidan Sarkin Fulani an saci kudi.

A makon nan kun ji cewa tabarbarewar tsaro ta kawo muhawara a Majalisar dattawa, har ana zargin gwamnati mai-ci da sakaci wajen tsare rai da dukiyar jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel