Batun tsige Shugaban Najeriya ya raba kan Sanatocin PDP da APC a Majalisar Dattawa

Batun tsige Shugaban Najeriya ya raba kan Sanatocin PDP da APC a Majalisar Dattawa

- Sanatocin PDP da na APC sun yi muhawara game da sha’anin tsaro a Majalisa

- ‘Yan Majalisar adawa suna ganin Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya gaza

- Sanatocin APC sun hakikance a kan cewa Gwamnati tana yin bakin kokarinta

A ranar Laraba, Sanatoci Biodun Olujimi (PDP, Ekiti) da Yusuf Yusuf (APC, Taraba), su ka samu sabanin ra’ayi a kan yunkurin tunbuke shugaban kasa.

Jaridar Punch ta ce ‘yan majalisar sun sha ban-bam kan maganar tsige shugaba Muhammadu Buhari saboda gazawarsa wajen shawo kan matsalar tsaro.

A makon da ya gabata, wasu Sanatocin jam’iyyar PDP sun ja-kunnen shugaban kasa ya tashi-tsaye, ko kuma majalisar tarayya ta dauki mataki a kansa.

KU KARANTA: Yadda za a magance matsalar rashin tsaro - Sanata Dickson

Amma Sanatocin APC mai mulki da rinjaye a majalisa, sun yi wa takwarorinsu raddi, suka ce babu bukatar hakan tun da gwamnati ta na bakin kokarinta.

Sanata mai wakiltar Ekiti ta Kudu a jam’iyyar PDP, Biodun Olujunmi, ta yi kira ga abokan aikinta da cewa, ka da su ji tsoron tsige shugaban kasa idan ta kama.

“Maganar tsige shugaban kasa ba ta zo ba tukuna. Idan an kawo batun, za mu yi ta kallon tsaf, saboda muna da matsalar gaske, dole mu fara neman mafita.”

A na ta ra’ayin, gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta yin abin da ya dace wajen kawo zaman lafiya.

Batun tsige Shugaban Najeriya ya raba kan Sanatocin PDP da APC a Majalisar Dattawa
Shugaban kasa da hafsun sojojin Najeriya Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rashin albashi da korar Ma’aikata 6, 000 ya jawo yajin aiki a Kaduna

Sanata Yusuf Yusuf na APC mai wakiltar yankin Taraba ta tsakiya bai yarda da Olujunmi ba, ya ce ko an tsige shugaban kasa, mataimakinsa ne zai karbi mulki.

A ganin Sanata Yusuf, da shugaban kasa da mataimakinsa, da shugaban majalisar dattawa, duk jirgi daya ya dauko su, tun da dai duk ‘ya ‘yan jam’iyya guda ne.

Olujimi wanda ta na cikin jagororin jam’iyyar hamayya ta soki salon mulkin gwamnatin APC, ta ce ana bukatar shugaban kasar da zai shiga, ya fita, a samu tsaro.

Gwamnonin APC sun amince da ra’ayin sauran abokan aikinsu a kan batun tsaro. Gwamnonin Kudun sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta canza salon rawarta.

Wadannan gwamnonin jihohi na kudancin Najeriya, ba su goyon bayan yadda gwamnatin tarayya ta ke tunkarar sha’anin tsaro da shirin sauya fasalin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel