Za a shiga yajin-aiki bayan Gwamnatin El-Rufai ta hana albashi, ta kori Ma’aikata 6000

Za a shiga yajin-aiki bayan Gwamnatin El-Rufai ta hana albashi, ta kori Ma’aikata 6000

- A ranar Litinin mai zuwa ma’aikatan jihar Kaduna za su tashi da yajin-aiki

- Ana zargin cewa rabon Gwamnatin jihar da biyan albashi tun watan Maris

- Kungiyar ta kuma zargi Gwamnatin Nasir El-Rufai da korar Ma’aikata 6000

Kungiyar kwadago ta reshen jihar Kaduna ta ce sama da ma’aikata 20, 000 da ake aiki a jihar, ba su samu albashin watan Afrilu da ya wuce ba.

Shugaban kungiyar NLC na Kaduna, Kwamred Ayuba Suileman, ya shaida wa jaridar Punch cewa ma’aikatan jihar za su tafi yajin aikin kwanaki biyar.

Kwamred Ayuba Suleiman ya ce za su fara wannan yajin aiki ne a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu, 2021, da nufin a ja-kunnen gwamnatin jihar.

KU KARANTA: Daya daga cikin Limaman ABU Zariya, Mustapha Qasim, ya rasu

Wani dalili da ya sa ma’aikatan za su tafi yajin aiki shi ne yadda gwamnati ta ke korar ma’aikata. NLC ta ce an kori ma’aikata sama da 6, 000 a Kaduna.

“Za a fara yajin-aikin a ranar Litinin zuwa Juma’a, a matsayin jan-kunne. Makasudin shi ne ana so gwamnati ta janye korar ma’aikatan jihar da take yi.”

Kwamred Ayuba Suleiman ya ce: “Ma’aikatan jihar ba su cikin jin dadi, ran su a bace. Gwamnati na yin ‘yar tinke, ta kori dul wanda ta ga dama daga aiki.”

“A lokacin da aka samu albashin watan Afrilu, ma’aikata 20, 000 a jihar ba su samu na su ba.”

KU KARANTA: Direba ya yi tatul da giya, ya murje 'Ya 'yan wani mutumi

Za a shiga yajin-aiki bayan Gwamnatin El-Rufai ta hana albashi, ta kori Ma’aikata 6000
Gwamna Nasir El-Rufai Hoto: @Elrufai
Asali: Twitter

Suleiman ya na sa ran gwamna Nasir El-Rufai zai janye matakin da ya dauka na sallamar mutane fiye da 6, 000 daga aiki, aka raba su da hanyar samunsu.

“Gwamnan ya na neman ya yi mana wahalar sha’ani, kuma dama a tarihinsa, bai da alaka mai kyau da kungiyoyin ‘yan kasuwa da ‘yan kwadago.” Inji NLC.

Shugaban kungiyar ya ce: “Za mu yi kokari mu jawo hankalinsa ta hanyar yajin-aikin, kuma mu na sa rai ya canza matsaya a kan sallamar ma’aikata 6, 000.”

A jiya aka ji Sanata mai wakiltar yankin yammacin Bayelsa, Seriake Dickson, ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya duba batun sake wa kasa fasali.

Seriake Dickson ya ke magana a kan kwamitin APC na sauya wa tsarin Najeriya zani da Nasir El-Rufai ya jagoranta, ya ce wannan aikin zai iya zama mafita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel