Gwamnonin Jihohin APC 7 sun soki yadda Gwamnatin Buhari ke tunkarar harkar tsaro
- Gwamnonin Jihohin Kudu sun hadu a kan lamarin tsaro ya na bukatar gyara
- Duka Gwamnonin jam’iyyar APC sun amince da ra’ayin sauran abokan aikinsu
- A wajen wani taro da aka yi a Delta, Gwamnonin ba su nuna sabanin siyasa ba
Premium Times ta ce gwamnoni bakwai daga cikin wadanda su ke mulki a karkashin jam’iyyar APC sun yi tir da salon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Jaridar ta ce wadannan gwamnonin na kudancin Najeriya, ba su goyon bayan yadda gwamnatin tarayya ta ke tunkarar sha’anin tsaro da sauya fasalin kasa.
Gwamnoni 15 na kudancin kasar nan suka halarci taron da aka yi a jihar Delta, inda suka tattauna a kan halin da kasa ta ke ciki, biyu daga ciki sun turo wakilansu.
KU KARANTA: Bayan sauya-sheka, ana rikici tsakanin Gwamnan Edo da Jam’iyya
Gwamnonin APC da aka yi wannan zama da su, sune: Babajide Sanwo-Olu, Gboyega Oyetola, Dapo Abiodun, Kayode Fayemi, Hope Uzodinma, da Dave Umahi.
Na karshensu shi ne gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, wanda ya zanta da manema labarai.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnonin sun nuna damu wa a game da halin tsaro da yake tabarbare wa, suka ba gwamnatin tarayya shawarwarin da za a bi.
Wadannan gwamnoni sun taru a kan cewa ya kamata mai girma Muhammadu Buhari ya fito ya yi wa al’umma jawabi, domin jama’a su gamsu da mulkin da yake yi.
KU KARANTA: An kai hari a Akwa Ibom, an kashe 'Dan Sanda
Bakin gwamnonin jihohin APC ya zo daidai da na sauran abokan aikinsu, wanda hakan zai bada mamaki ganin suna jam’iyya guda da shugaba Muhammadu Buhari.
Babu wani gwamnan APC ko daya da aka samu bai goyi bayan matakan da aka dauka a taron da aka yi a Asaba ba. Kan gwamnonin APC, PDP da APGA duk ya hadu.
Rotimi Akeredolu wanda ya na cikin manyan APC, ya sanar da ‘yan jarida cewa duka gwamnonin Kudu, sun goyi bayan matsayoyin da aka cin ma a wajen wannan taro.
Dazu aka ji Sanata mai wakiltar yankin yammacin Bayelsa, Seriake Dickson, ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya duba batun sake yi wa Najeriya fasali.
Sanatan yake cewa ta kare wa Gwamnonin jihohi, ya fada wa gwamnatin tarayya cewa abin da ya kamata ta yi shi ne ta duba aikin da kwamitin gwamna El-Rufai ya yi.
Asali: Legit.ng