Dalilin da ya sa mukayi Sallar Idinmu a ranar Laraba, Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Dalilin da ya sa mukayi Sallar Idinmu a ranar Laraba, Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana dalilin da ya sa ya jagoranci Sallar Idi a ranar Laraba duk da cewa hakan ya sabawa umurnin mai alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Abubakar Sa'ad.

Legit ta ruwaito muku cewa wasu sun gudanar da Sallar Idinsu yau duk da sanarwan Sarkin Musulmi, wanda shine jagoran Musulmin Najeriya cewa sai ranar Alhamis saboda rashin ganin jinjirin wata.

Amma Sheikh Dahiru Bauchi bayan Sallar Idi a gidansa dake Bauchi, ya ce an ga watan Shawwal ranar Talata.

A cewarsa, an wata a wurare irinsu Gombe, Gadau da Kebbi.

"Bisa rahotannin da muka samu cewa an ga wata, abinda mutum biyu ko jama'a suka shaida ya isa," Shehi yace.

"Shi yasa muka zo Sallar Idi saboda watan Ramadana ya kare, an shiga watan Shawwal ."

Dalilin da ya sa mukayi Sallar Idinmu a ranar Laraba, Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Dalilin da ya sa mukayi Sallar Idinmu a ranar Laraba, Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Wakilin Legit ya samu tattaunawa da babban Malami, Sheikh Muhammad Auwal Maishago Zaria, kan matsayar addini kan wadanda sukayi Sallarsu a yau sabanin sanarwan Sarkin Musulmi.

Sheikh Maishago ya bayyana cewa wannan kuskuren kuma yunkurin rana kan al'umma wanda ya sabawa ka'idojin addinin Musulunci.

Yace: "Duk abinda zamu yi da ya shafi addini, Annabinmu bai bar duniya ba sai da ya fada mana yadda zamuyi, kuma ya umurcemu da biyayya da abinda shugabannin suka akai ko da ko wasu irin shugabanni za'a iya samu a gaba. Kuma a hakan yace mu musu biyayya kan abubuwan da basu sabawa dokokinshi ba"

"Shi kuma sanarwan Sarkin Musulmi a abinda muka lissafa dangane da nassoshin annabi bai sabawa abinda shi Annabin yace ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel