Guardiola ya samu nasarar da Alex Ferguson ya yi shekara 27 kafin ya samu a Manchester

Guardiola ya samu nasarar da Alex Ferguson ya yi shekara 27 kafin ya samu a Manchester

- Manchester City ta doke Tottenham a gasar cin kofin EFL a filin wasan Wembley

- Pep Guardiola ya cin ma nasarar da Alex Ferguson ya yi shekara 27 kafin ya kafa

- Kungiyar ta yi shekaru hudu ta na cin kofin, abin da Liverpool ta taba yi a tarihi

A ranar Lahadin nan ne kungiyar Manchester City ta sake samun nasarar cin gasar kofin EFL watau Carabao a filin wasan kwallon kafa na Wembley.

Wannan gagarumar nasara ta na nufin Manchester City ta shafe shekaru hudu a jere ta na lashe gasar karamin kofin, abin da Liverpool ta taba yi a 1980s.

Kungiyar Manchester City ta samu nasarar ta na farko a wannan shekarar ne bayan ta doke Tottenham da ci 1-0 a wasan da aka buga a ranar Lahadin.

KU KARANTA: Mourinho ya zama Kocin da kungiyoyi 3 su ka tsige a kasar Ingila

‘Dan wasa Aymeric Laporte ne ya yi sanadiyyar da Man City ta lashe gasar bayan ya jefa kwallo da kai bayan an kai minti 80 babu wanda ya zura kwallo.

Yayin da Tottenham da ta samu sabon koci ta ke kokarin karya mummunan tarihin da ta ke da shi na cin kofi, City ta na harin lashe gasar ne a wani karo.

‘Yan wasan Pep Guardiola sun nuna kwarewarsu a wannan wasa na cin kofi, musamman a zangon farko, tun a wannan lokaci ya kamata a jefa kwallaye.

Saura kiris Tottenham ta kai labari a zango na biyu bayan Lucas Moura ya kai wa ‘dan wasan kasar Argentina, Lo Celso, wani kwallo mai hadarin gaske.

KU KARANTA: Tauraron Super Eagles ya bada gudumuwar kudi a gina masallaci

Guardiola ya samu nasarar da Alex Ferguson ya yi shekara 27 kafin ya samu a Manchester
Pep Guardiola da Alex Ferguson Hoto: www.goal.com/en-ng
Asali: UGC

Ikay Gundogan da Riyad Mahrez sun yi wasa da damar da su ka samu a wasan kafin Laporte ya cin ma kwallon De Bruyne ya kawo bayan an yi wa City keta.

Da wannan nasara, Pep Guardiola ya na da kofin EFL wanda yaka canza wa suna zuwa Caraabao har hudu, daidai da Sir Alex Ferguson da kuma Jose Mourinho.

Kwanakin baya kun ji Jose Mourinho zai tashi da Naira Biliyan 8 a asusunsa bayan Tottenham ta sallame shi daga aiki ana daf da buga wasan cin kofin EFL.

Yayin da Sir Alex Ferguson ya shafe shekaru 27 a kungiyar Manchester, an kori Mourinho daga aiki a kungiyoyin Chelsea, Manchester United da Real Madrid.

Asali: Legit.ng

Online view pixel