Mummunar kaddara ta aukawa iyalin wani mutum, mota ta murkushe masa Yara har 4
- Wata mota ta dura kan mutane 4 ‘yan gida daya a a Agege, jihar Legas
- Mutum uku daga cikin hudun da aka buge sun bakunci gidan barzahu
- Ana zargin direban ya dirki giyansa ne kafin ya fara tuki a kan hanya
Jaridar Daily Trust ta ce an nemi ayi 'yar hatsaniya sa’ilin da wani direban babbar mota ya murkushe wasu yara da suka fito daga gidan mutm daya.
Wannan musiba ta auku ne a unguwar Agege da ke garin Legas a karshen makon da ya wuce.
Kamar yadda mu ka samu labari, nan-take mutum biyu daga cikin wadanda aka buge suka mutu, ragowar gudan ne ya cika bayan kama hanyar zuwa asibiti.
KU KARANTA: Bikin sallah: An baza 'Yan Sanda sama da 3000 a Imo
Mutum na karshe da direban ya buge yana cikin wani mummunan hali a asibiti. Har zuwa yanzu, ba mu samu labarin wani asibiti aka kai wannan mutum ba.
Ana zargin cewa direban wannan mota ya yi shaye-shaye ne kafin ya hau titi, sannan ya rika gudun ganganci, hakan ya yi sanadiyyar rasa rayukan jama’a.
Wani mutumi wanda ya samu labarin abin da ya faru, ya ce an yi hadarin ne a wani mummunan tsukukun titi da ke Alfa Nla a Oniwaya, a cikin unguwar Agege.
Mutanen da su ka lura da abin da ya faru, sun fita a fusace sun kamo direban, suka kusa hallaka shi, kafin jami’an ‘yan sanda na kwana-kwanan RSS su ceto shi.
KU KARANTA: Jama'a suka jawo matsalar Boko Haram da ‘Yan bindiga - Sanata
Duk da haka, wasu masu zaman banza sun fasa madubin wannan babbar mota da ake zargin direban ta ya yi makil da giya, ya hau hanya ya na ta faman layi.
“Abin ya faru ne a kusa da gida na, gidaje biyu kafin a kai gida na, ya murkushe wadannan yara.” inji wani makwabcin mutumin da wannan musiba ta auka masa.
“Matan biyu sun mutu nan-take, na karshe ya rasu kafin a kai asibiti. Su hudun duk ‘ya ‘yan mutum guda ne. Zo ka ga mutum a kwance, kwakwalwa a kan titi.
Kun ji yadda 'Yan sandan jihar katsina su ka damke wasu mutum hudu da ake zargin suna cikin 'yan bindigan da suka gallabi yankin garin Kankara da kewaye.
Kamar yadda muka samu rahoto, bayan bayanan sirrin da hukumar 'yan sandan suka samu, sun tare 'yan bindigan, sannan suka karbe shanu 170 da tumaki 38.
Asali: Legit.ng