Jami’ar ABU da mutanen Zaria sun yi rashin babban Limaminsu a daren karshen azumi
- Daya daga cikin Limaman ABU Zaria, Dr. Mustapha Isa Qasim, ya rasu
- Marigayin ya rasu ne bayan ya yi ta jinyar rashin lafiya a ABUTH Shika
- Mustapha Isa Qasim ya dauki shekara da shekaru ya na koyar da addini
A daren Laraba, 12 ga watan Mayu, daya daga cikin limaman jami’ar Ahmadu Bello, Mustapha Isa Qasim, ya rasu ya na da shekara 60.
Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Dr. Mustapha Isa Qasim ya rasu ne bayan ya shafe kusan mako guda ya na ta fama da jinyar rashin lafiya.
‘Yanuwan Marigayin sun tabbatar mana da rasuwar malamin boko da addinin musuluncin a asibitin koyon aiki na ABUTH da ke Shika.
KU KARANTA: Tarihin limamin ABU, Abubakar Musa Imam
Kafin rasuwarsa, Mustapha Isa Qasim, mataimakin Farfesa ne a sashen koyar da addinin musulunci a jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria.
Marigayin ya shafe shekaru kimanin 30 a ABU Zaria, ya taba rike makarantar koyon musulunci da ilmin shari’a da ke garin Misau, jihar Bauchi
Shugaban kungiyar daliban Najeriya na reshen jihar Kaduna, Dr. Shehu Salihu Umar ya sanar da mutuwar a shafinsa na Facebook, yake cewa:
“Innalillahi wa inna ilahi raji'un! Mun rasa Dr. Mustapha Isa Qasim, Limamin manyan masallatan ABU da ITN Zaria.”
KU KARANTA: Yaron Sheikh Jafar Adam ya haihu, ya maida sunan Mahaifinsa da aka kashe
Shehu Salihu Umar ya roki Ubangiji ya yi wa wannan ta’alaki rahama, ya ce ‘Inna lillahi wa inna ilahi raji'un! Yau ranar bakin ciki ce a wurinmu."
Bayan limancin da malamin yake yi a wadannan masallatai, ya dauki shekaru kusan 40 ya na koyar da addinin musulunci a garin Zariya, jihar Kaduna.
Za ayi jana’izarsa a ranar 30 ga watan Ramadan da karfe 1:30 na rana a jami'ar. Mustapha Isa Qasim ya bar mata uku, ‘ya ‘ya 17, da jikoki masu yawa.
A shekarar bara ne aka ji cewa daya daga cikin limaman farko na fitacciyar jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke Zariya, Imam Abubakar Musa ya rasu.
A ranar Lahadi, 19 ga Watan Junairun 2020, Limamin ya rasu ya na da shekaru kusan 110. Imam ya rasu, ya bar Mata biyu da ‘Ya ‘ya 46 da kuma jikoki rututu.
Asali: Legit.ng