Rikicin gida: ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun kai karar Gwamnan Edo gaban Shugabannin PDP

Rikicin gida: ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun kai karar Gwamnan Edo gaban Shugabannin PDP

- Majalisar SWC ta jihar Edo ta kai karar Gwamna Godwin Obaseki

- Shugabannin PDP sun aika takarda zuwa ga Prince Uche Secondus

- Ana kukan Obaseki yana tafiya ne da ‘Yan APC kawai a gwamnati

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa jam’iyyar PDP ta reshen jihar Edo, ta kai karar gwamna Godwin Obaseki zuwa wajen majalisar NWC a Abuja.

Wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar ta PDP sun bukaci mataimakin gwamnan jihar Edo, Mista Philip Shaibu, ya yi murabus, a matsayin yarjejeniyar da aka yi a baya.

Shugabannin gudanarwa na PDP na Edo sun aika takarda zuwa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, da sa hannun Dr. Tony Aziegbemi.

KU KARANTA: NPA ta na facaka da biliyoyi duk shekara - Minista

Tony Aziegbemi da sakatarensa, Hillary Otsu da sauran ‘yan majalisar jihar Edo sun zargi Godwin Obaseki da kokarin ruguza daukacin shugabannin jihar.

An aika wannan wasika ne bayan zaman da shugabannin PDP na reshen Edo suka yi a ranar Litinin.

Aziegbemi ya sanar da abokan aikinsa cewa gwamna Obaseki da wasu kusoshin gwamnatinsa sun yi zama da nufin sauke duka shugabanninn PDP na Edo.

Bayan tsawon lokaci ana wannan taro, majalisar SWC da shugabannin kananan hukumomi sun nuna ba su yarda da abin da gwamnan yake neman yi ba.

Rikicin gida: ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun kai karar Gwamnan Edo gaban Shugabannin PDP
Gwamnan Edo, Godwin Obaseki
Asali: Facebook

KU KARANTA: EFCC ta karbo dukiya daga hannun Alison Madukwe

Shugabannin jam’iyyar mai mulki sun gargadi majalisar koli ta NEC cewa ruguza shugabannin PDP da aka zaba, zai saba wa umarnin Alkalin kotu.

SWC ta ce rukuni uku ne su ka jawo wannan rikici, da masu harin zabe mai zuwa, da wadanda su ka sha kasa a zaben fitar da gwani da kuma wasu iyayen gida.

Daga cikin wadanda ake zargi akwai; Dr. Raymond Dokpesi, Mike Oghiadomhe da Tom Ikimi.

Kafin yanzu, kun ji Jam’iyyar PDP ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da shugabar NPA, Hadiza Bala Usman.

PDP ta bukaci Buhari ya tattara Amaechi da Bala Usman a tsige a kan zargin satar kudin jama'a, ta ce gwamnatin APC ta maida Hukumomin Gwamnati ATM.

Asali: Legit.ng

Online view pixel