Labari na musamman: Tarihin Marigayi Abubakar Musa Imam

Labari na musamman: Tarihin Marigayi Abubakar Musa Imam

Kwanakin baya ne aka yi rashin babban Malamin da ya yi shekara da shekaru ya na Limancin jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Imam Abubakar Abubakar Musa.

Legit.ng Hausa ta samu yin hira da Iyalin Marigayin ta bakin babban Dansa a cikin maza, Dr. Sa’id Abubakar Abubakar Musa, wanda ya ba mu tarihin Mahaifin na su.

Haihuwa

An haifi Imam ne a wani wuri da ake kira Dan-kande da ke cikin Kauyen Ruwan Dorawa, karkashin karamar hukumar Anka da ke jihar Sokoto. A yanzu wadannan Garuruwan su na cikin Karamar hukumar Maru a Jihar Zamfara a shekara ta 1892. Wannan ya na nufin ya bar Duniya ya na da shekaru 127.

Karatu da koyarwa

Marigayin ya fara karatu ne a Dan-kande wurin Limamin kauyen. Bayan saukar Alqurani mai girma, ya ci gaba da karatun sauran littafan addini wurin Limamin Juma’a na garin Ruwan-doruwa. Shehin yayi karatu wurin wani babban Malami a Kauyen Gusau da ake kira Rijiya. Domin kokarin neman ilmi, sai Marigayin ya yi tattaki zuwa Garin Bilbis a wurin wani Malam Aliyu Babba na Bilbis. Daga bisani, Imam ya koma garin ‘Yandoton-Daji domin karantarwa. Tafiya ba tayi nisa ba har daliban da ma Sarkin Garin su ka fahimci cewa shine ya kamata ya zama Limamin Juma’a na Garin, saboda haka Sarkin garin ‘Yandoton-Daji ya bukace shi da ya dauki wannan nauyi, amma shi kuma ya ce ba zai iya ba. Mai Garin ya kara samunsa a daren wata Juma’a bayan mako daya kuma ya kara nanata masa bukatar al’umma na ya zama Limamin Juma’a. Wannan ya sa Malamin ya yi assubanci tare da manyan Dalibansa su ka bar Garin ‘Yandoton-daji da Assubahin Juma’a; kuma basu zame ko ina ba sai a wani gari da ake kira Sheme kusa da Funtua. Wani Malami da ya yi fice a Garin shi ne sanadiyyar zuwansu Sheme. Amma bayan sun isa Garin, sai Malamin ya fahimci iyaka zurfin iliminsa. Saboda haka ya bukace shi da ya zauna tare da shi domin su rika koyar da mutane kuma shi ma ya kara karatu a wurin Marigayin. Imam ya yarda da wannan shawara. Can kuma samu labarin wani shahararren Malami a Funtua, Malam Mustafa Imam Funtua. Bai yi kasa a guiwa ba, ya isa Funtua ya kuma nemi ya koyi ilmin harshe wurinsa. Malam Mustafa ya yi masa jagora zuwa wurin wani babban Malami da ke Katsina mai suna Malam Mai Dala’ilu domin samun ilmi mai zurfi na harshen Arabi. Bayan ya kamala karatunsa sai Malamin ya hada shi da wasu dalibai domin su yi karatu a wurinsa. Daga nan Imam Abubakar ya isa garin Tudun-Wadan Zariya domin ya kara samun ilmin karatun litattafan lugga kamarsu ‘Shu’ara da Muqama’ da kuma manyan littatafan ilmin Fiqihu wurin Malam Musa Zariya. Daga nan Imam Abubakar ya isa garin Jos sakamakon labarin wani Alkali kuma babban malami da ya ji labarinsa mai suna Alkali Jibril. Amma wannan Alkali ya umurcesa da ya koma Zariyar da ya baro domin akwai duk ilmin da ya ke nema a can. Daganan Imam ya shiga Garin Dokar Dan Sambo a cikin Jihar Kaduna. A nan ma an bukaci ya zama babban Limamin Juma’a, amma ya ki karbar wanna tayi, a dalilin haka ya sanar da Almajiransa cewa zai yi kaura zuwa Unguwar Marmara da ke Sabon-Garin Zaria.

KU KARANTA: An wulakanta Iyalin Muhammadu Sanusi II bayan an tsige sa

Labari na musamman: Tarihin Marigayi Abubakar Musa Imam
Tsohon Limamin Jami'ar ABU Marigayi Abubakar Musa Imam
Asali: Facebook

Jami’ar ABU Zariya

Bayan dawowarsa Zariya, ana cikin wannan hali, sai aka bukaci samun malami da zai rika koyarda ‘Ya ’yan maikata da kuma dalibai na jami’ar Ahmadu Bello. Daga cikin wadanda aka wakilta domin su nemo malamin akwai irin su Marigayi Alhaji Abdullahi Muhammad Dewu, Alhaji Ahmadu Doso, Alhaji Ciroma da sauransu. Wadannan wakillan Jami’a sun tuntubi Imam Abubakar akan wannan bukata, daga farko Malam bai so ya amsa ba domin ba ya son ya tafi ya bar Dalibansa, amma daga baya aka lallabe shi. Dalilin wannan koyarwar a Jami’a ya hadu da Limamin Jamiar na wancan lokaci (Malam Basakkwace). Har dai Limamin ya nemi Malamin ya taimaka masa ya zama Limami na wucin-gadi lokacin da tafiyar aikin Hajji ta kama Limamin da Na’ibinsa. Malam ya zama limamin rikon kwarya har zuwa lokacin da Allah ya nufesu da dawowa. Bayan dowawarsu, Malam Basakkwace ya gamu da hadari akan hanya wanda ya yi sanadiyyar rasuwarsa. Hakan ya sa Marigayi ya zama Naibi na daya ga Farfesa Abdullahi Muhammad. Bayan shekara daya, tafiya ta kama Farfesa Abdullahi zuwa kasashen waje domin neman karin karatu. Sakamakon haka Malam ya kara zama Liman na rikon kwarya. Bayan dawowar Farfesa sai Farfesa ya roki Shehin ya cigaba da limanci. A haka ne Malam Imam Abubakar ya samu kansa a matsayin limamin masallacin A.B.U Zaria. Daga nan ya kasance ya na yin Sallar Juma’a a duk mako kuma yana halartar salloli biyar. Bugu da kari, Imam Abubakar ya cigaba da koyarwar da ya saba. Ya kan dauki darussa ne tsakanin Azahar da La’asar da kuma tsakanin Magriba da Isha’i har ga manya.

Shugabanci

Malam ya cigaba da lura da Dalibai da Malamai na jami'ar ta hanyar nasiha ta hikima. Irin wannan wannan jagoranci da shugabanci na sa ya mamaye Garuruwan Zariya da kuma Masarautunsu. Wannan ya jawo masa karbuwa wurin al’umma daban-daban. Lokutta da dama Malam ya kan sansanta Dalibai da hukumar makaranta, ya kan shiga tsakanin Malamai da hukukumar makaranta da kuma tsakanin malamai su kansu; Kai har ma tsakanin miji da mata ko Da da Mahiafi. A cikin Garuruwan Zazzau kuwa ya sasanta Limamai da alummarsu da kuma tsakanin junan Malamai. Saboda kokarinsa na zaman lafiya da mutane, har karshen rayuwarsa bai taba kai karan wani wurin hukuma ba kuma ba’a taba kai karansa ba. Ya kan warware rikici salin-alin.

Iyali

Game da Iyali kuwa, Malam ya bar Mata uku da Yara ‘Ya ‘ya 46. Daga ciki akwai Maza 24 da Mata 22. Haka zalila ya bar jikoki da dama.

Allah ya jikinsa da rahama.

Legit.ng Hausa ta yi hira da Dr. Sa’id Abubakar Abubakar Musa a Ranar 26 ga Watan Junairun 2020 a Zariya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel