Babban Limamin Jami’ar A.B.U Zariya, Imam Abubakar Musa ya rasu

Babban Limamin Jami’ar A.B.U Zariya, Imam Abubakar Musa ya rasu

Mun samu labari cewa Dattijon Limamin fitacciyar jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke Zariya, Malam Imam Abubakar Musa ya bar Duniya.

Ubangiji ya karbi ran wannan Bawan Allah ne a Ranar Lahadi, 19 ga Watan Junairun 2020. Limamin ya rasu ne da yammacin wannan rana.

Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa an bizne shi da kimanin karfe 7:00 na yamma, bayan an yi masa sallar jana’iza a cikin jami’ar a Samaru.

Da farko sanarwa ta zo cewa za ayi wa tsohon Limamin sallah ne bayan Isha’i, amma daga baya aka canza tsari aka yi nasa jana’iza bayan Magriba.

Daruruwan mutane su ka samu halartar wannan jana’iza da ta gudana a filin idi da ke Kudancin katafaren masallacin Juma’ar cikin jami’ar.

KU KARANTA: Yadda Sojoji su ka kashe Firimiyan Arewa Ahmadu Bello cikin Watan azumi

Babban Limamin Jami’ar A.B.U Zariya, Imam Abubakar Musa ya rasu
Marigayi Imam Abubakar Musa a shekarun baya
Asali: Original

Daya daga cikin manyan ‘Ya ‘yan Marigayin wanda shi ma Limami ne a Makarantar watau Imam Sa’ad Abubakar, shi ne ya yi masa salla da kansa.

Daga cikin wadanda su ka halarci sallar nan akwai shugaban jami’ar, Farfesa Ibrahim Garba da mataimakinsa, Farfesa Sadiq Zubairu Abubakar.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Marigayin ya rasu ne ya na da shekaru 110 a Duniya, kuma ya bar Mata biyu da ‘Ya ‘ya 100 da jikoki fiye da 100.

A wata sallar idi da Marigayin ya yi kafin ya fara jinya, ya bayyana cewa Sardauna Ahmadu Bello ya nada shi limanci tun a wancan shekarun baya.

Daga cikin ‘Ya ‘yan da ya bari akwai tarin Mahaddata irin su Imam Sa’ad da Dr. Yusuf Abubakar Imam wadanda duk Malamai ne a wannan jami’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel