Hukumar NPA karkashin Hadiza tana watandar N50bn kowace shekara, Ma'aikatar Sufuri

Hukumar NPA karkashin Hadiza tana watandar N50bn kowace shekara, Ma'aikatar Sufuri

- Ministan Sufuri Amaechi na cigaba da bayyana dalilan da yasa aka dakatad da Hadiza

- Shugaba Buhari ya kaddamar da kwamiti na musamman na bincikenta

- Wannan ya biyo bayan saka nada ta a wa'adi na biyu a 2021

Ma'aikatar Sufuri a ranar Talata ta bayyana sabbin hujjoji domin gudanar da bincike kan bazakalar da ake zargin an yi a hukumar tashohin jiragen ruwan Najeriya NPA karkashin Hadiza Bala Usman.

Sakatariyar din-din-din na ma'aikatar, Magdalene Ajani, a jawabin da ta sake ta ce hukumar NPA ta yi almubazzarancin kudade tare da bayar da kwangilar wasu ayyukan da za'a iya yi a cikin gida irinsa yasa, rahoton DT.

"Hukumar NPA na almubazzaranci kudaden jama'a inda ta ke kashe sama da bilyan 50 a kowace shekara kan kwangilolin da za ta iya sayan kayan aiki tayi da kanta," Jawabin yace.

Ajani tace a duk lokacin da wa'adin kwangilan ya kare, ma'aikatar kan bukaci korarriyar shugabar NPA. Hadiza Bala Usman, tayi bayani kan nasarorin da aka samu kafin sake bayar da wani amma tayi kunnen jaki.

"Shekara da shekaru hukumar NPA na bada wadannan kwangilolin na kudin N50bn-N60bn a kowace shekara," ta kara.

KU KARANTA: Mun Ƙwato Dala Miliyan $153M Daga Tsohuwar Ministan Man Fetur, Bawa

Hukumar NPA karkashin Hadiza tana watandar N50bn kowace shekara, Ma'aikatar Sufuri
Hukumar NPA karkashin Hadiza tana watandar N50bn kowace shekara, Ma'aikatar Sufuri Hoto: @thecable
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnati Ta Amince da Daya Daga Cikin Bukatun Likitocin Najeriya

Kun ji cewa an dakatad da shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa a Najeriya NPA, Hadiza Bala Usman, domin bada dama don gudanar da bincike kan wasu kudaden da ake zargin ba'a sanya a asusun bai daya ba.

Wasu takardu da Legit Hausa ta gani sun nuna yadda Ministan Sufuri yayi zargin badakalar N165bn.

A bisa wasikar da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya aikewa shugaba Buhari, ya ce adadin kudaden ya kamata ace hukumar NPA ta tura asusun gwamnatin tarayya tsakanin 2016 da 2020 basu kai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel