Bayan shekaru fiye da 60, Sabon Sarkin Zazzau ya dawo da idi zuwa filin Mallawa
- Wannan shekarar Zazzagawa za su yi sallar idi ne a filin Mallawa
- An samu wannan sauyi ne bayan mulki ya koma hannun Mallawa
- A tarihi kowane gidan sarauta suna da wurin da su ke yin sallar idi
Rahotanni daga Daily Trust sun bayyana cewa wannan karo an samu sauyi game da wurin da za a gudanar da sallar idin karamar sallah a Zaria.
Wannan shekara, Mai martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli zai yi sallah ne a babban filin idin Mallawa da ke hanyar Zaria zuwa garin Jos.
A kasar Zazzau, kowane gidan sarauta ya na da wurin da yake gudanar da sallar idi a tarihi.
KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya durkusa a gaban Sarki Ahmad Bamalli
Wannan ne karon farko da mutanen Zazzau za su fita zuwa wani fili dabam da na Kofar Doka domin gudanar da sallar idi a cikin shekaru 62.
Kafin Mai martaba Sarki Ahmed Nuhu Bamalli, ya dare gadon sarauta, sarakunan bayansa sun yi idi ne a wani wuri da ke yamma da filin mallawa.
Wani babban jami’in fadar Sarkin Zazzau, Alhaji Abubakar Ladan, ya tabbatar wa ‘yan jarida wannan shekara za ayi sallah ne a filin mallawa.
Sarakunan Zazzau Muhammad Aminu, da Shehu Idris wanda su ka fito daga gidan Katsinawa sun shafe shekaru 62 suna yin sallah a Kofar Doka.
KU KARANTA: Sallar Juma'ar farko da Sarki Ahmed Nuhu Bamalli ya yi
Wanda aka haifa shekaru 60 da suka wuce bai taba samun sallar idi a filin mallawa ba. Dawowar sarautar zuwa gidansu ya canza abubuwa a bana.
Legit.ng Hausa ta samu labari ana ta shirye-shiryen bikin sallah a Zaria, inda ake ganin ana wuce wa da abincin dabbobi daga nesa zuwa fadar Sarki.
Ana rade-radin wannan karo za ayi hawa na musamman a Zazzau, ganin wannan ce sallar farko da Mai martaba Ahmad Bamalli zai yi a gadon mulki.
Idan za ku tuna, a ranar 7 ga watan Oktoba, 2020, gwamnatin Kaduna ta tabbatar da Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.
Kakaninsa Malam Musa su ne su ka kafa sarautar kasar Zazzau bayan jihadin Shehu Danfodio. Mahaifinsa Magajin Gari, Nuhu Bamalli ya rasu a 2001.
Asali: Legit.ng