Bidiyon El-Rufai ya durkusa a gaban Sarki Ahmad Bamalli ya janyo cece-kuce
- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya durkusa wa sabon sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli
- A wani Bidiyo da yayi ta yawo a Twitter, an ga Gwamnan ya durkusa wa sarkin yana gaishe shi
- Bayan ganin Bidiyon, mutane da dama sun yi ta yaba wa gwamnan akan rashin girman kansa
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya durkusawa sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba don nuna girma da darajar sarkin.
Wani shafin kafar sada zumuntar zamani na Twitter mai suna Zazzau Emirate, sun wallafa bidiyon gwamnan a durkushe gaban sarkin, wanda dama haka al'adar Hausa-Fulani tazo.
Idan ba'a manta ba, marigayi sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya rasu ne a ranar 20 ga watan Satumba, bayan yin shekaru 45 yana mulkar masarautar.
Bayan rasuwarsa ne aka nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, wanda ya maye gurbin sa, a matsayin Sarkin Zazzau na 19.
Bamalli ya zama sarkin Zazzau na farko a cikin shekaru 100, tun bayan rasuwar kakansa, Sarki Alu Dan Sidi a shekarar 1920.
Wadanda suka kalli Bidiyon sunyi mamakin irin rashin girman kan Gwamnan jihar Kaduna, a matsayinsa na mai fadi aji a jihar, har ya durkusa a gaban sabon Sarkin.
KU KARANTA: Kada ku sa mu yadda cewa wadanda aka lallasa a zaben 2019 ne suka bullo da EndSARS - Hadimin Buhari ga dan Atiku
KU KARANTA: EndSARS: Hotunan mata 6 'yan gwagwarmaya da suka dauka hankali
A wani labari na daban, an nada sarki Bamalli a matsayin sarkin zazzau na 19, a ranar 7 ga watan Oktoban 2020.
An maye gurbin marigayi Dr Shehu Idris, wanda ya rasu a ranar 20 ga watan Satumbar 2020, bayan yayi shekaru 45 akan karagar mulki.
Sarki Bamalli ne sarki na farko daga gidan mallawa cikin shekaru 100, tun bayan rasuwar kakansa Sarki Alu Dan Sidi, wanda ya rasu a 1920, kamar yadda masana tarihi suka sanar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng