Bidiyon sallar Juma'a ta farko ta Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli
- A yau Juma'a ne sabon Sarki Alhaji Ahmed Bamalli ya yi sallar Juma'a ta farko bayan nadinsa
- Karagar mulkin masarautar ta kwashe tsawon kwanaki babu sarki tun bayan mutuwar Shehu Idris
- A ranar 7 ga watan Oktoban 2020 ne Gwamnan jihar Kaduna ya nada Bamalli a matsayin sarkin Zazzau
A Yau Juma'a, 10 ga watan Oktoban 2020 ne sabon sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya yi sallar Juma'a ta farko bayan nada shi da aka yi.
Gwamnan jihar kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau na 19 bayan rasuwar Balaraben Dakta Shehu Idris.
Manyan masu sarauta a masarautar Zazzau sun yi mubaya'a ga sabon sarkin.
Tun bayan nada sabon sarkin, ya shiga fadar masautar cike da murna tare da farin cikin sarautar da ta koma gidan Mallawa wacce ta barsu tun shekaru 100 da suka gabata.
Tun bayan rasuwar kakan sarkin, marigayi Sarki Aliyu Dan Sidi a 1920, sarauta bata sake komawa gidan ba.
Alhaji Ahmed Bamalli ya kafa babban tarihi daga gidan Mallawa.
KU KARANTA: Dakarun soji sama sun ragargaji 'yan bindigar daji a Kaduna
KU KARANTA: Ambaliyar ruwa: Rayuka 36 sun salwanta, mutum 470 sun rasa gidajensu
A wani labari, 'yan majalisar nadin sarakunan Zazzau sun amince da zabar Ahmed Bamalli a matsayin sarkin Zazzau, babu dadewa da nada shi.
An nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoban 2020. Bayan rasuwar Sarki Shehu Idris da yayi shekaru 45 a karagar mulki (1975-2020).
Jim kadan bayan Sakataran Gwamnatin jihar Kaduna ya isa fadar sarkin Zazzau da sanarwar nadin sabon sarkin, 'yan uwa da abokan arziki da al'ummar Zazzau suka yi ta tururuwar zuwa fada farin ciki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng