Dangote Group na barazanar shiga kotu kan zarginsa da hannu a badakala da Hukumar NPA

Dangote Group na barazanar shiga kotu kan zarginsa da hannu a badakala da Hukumar NPA

- Kamfanin Dangote Group ya musanya rahoton samun alaka da Hukumar NPA

- Wani babban Jami’in kamfanin ya ce babu wani abin da ya hada su da ICTSI

- Anthony Chiejina ya nuna akwai yiwuwar su shiga kotu a kan wannan rahoto

A wani jawabi da kamfanin Dangote ya fitar a ranar Litinin, 10 ga watan Mayu, 2021, ya nesanta kansa daga karbar kwangiloli a hukumar NPA.

The Cable ta rahoto cewa babban jami’in yada labarai na kamfanin Dangote Group, Anthony Chiejina, ya maida martani kan rade-radin da ke yawo.

Mista Anthony Chiejina ya ce ana yada wannan jita-jita ne saboda a bata masa sunan kwaransu.

KU KARANTA: Bani da ikon bada kwangila ni kadai a NPA - DG

“Hankalinmu ya zo kan wani rubutu da aka buga a shafin yanar gizo na Sahara Reporters da taken: ‘EXCLUSIVE: How Suspended NPA Boss, Hadiza Usman Awarded Coastline Terminals To Dangote’s Proxy Company In Shady Deal.”

Ya ce: “Mu na so mu zayyana cewa babu hadin kamfanin Dangote Group ko ta kusa, ko ta nesa da ICTSI, kamar yadda aka nemi a nuna a wannan rubutun.”

“Dangote Group ya musanya wannan rahoto da aka fitar kacokam dinsa, tare da yin tir da yunkurin gan-gan na Sahara Reporters da nufin cusa hannunmu a cikin abin da bamu san kan sa ba.”

Kamfanin na Dangote ya tabbatar da cewa bai da wata alaka da tashan ruwan Onne, kuma bai shiga kowace irin yarjejeniya da hukumar NPA ta kasa ba.

KU KARANTA: Amaechi ya kafa kwamitin da zai binciki Bala Usman

Dangote Group na barazanar shiga kotu kan zarginsa da hannu a badakala da Hukumar NPA
Hadiza Bala Usman Hoto: Facebook/Hadiza Bala Usman kallabi tsakanin rawuna
Asali: Facebook

Haka zalika kamfanin na Aliko Dangote ya ce bai san da maganar ICTSI da ake zarginsa da su ba.

Za a iya tabbatar da wannan matsaya daga wasikar da babban jami’in kamfanin ICTSI, Hans-Ole Madsen, ya aika wa jaridar Sahara Reporters inji Chiejina.

"Hans-Ole Madsen ya sanar da jaridar cewa ICTSI kamfanin kasar Philippine ne da ke aiki a tashoshin ruwan Duniya, wanda bai da alaka da Dangote."

A karshe Chiejina ya ce kamfaninsu na tuntubar sashensu na shari’a domin sanin matakin da za a dauka kan wannan kazafi da labarin kage da aka yi masu.

A ranar Litinin ne ku ka ji cewa wasu daga cikin 'Yan majalisar sun yi kira ga EFCC da ICPC su binciki zargin badakalar da ke wuyan Hadiza Bala Usman.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar tarayya, Hon. Ndudi Elumelu ya fito ya na cewa ya kama EFCC ta cafke Hadiza Bala Usman, ta fara shirin gurfanar da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel