Hadiza Bala Usman ta na cikin sabuwar matsala, Majalisa ta fara gayyato mata Hukumar EFCC

Hadiza Bala Usman ta na cikin sabuwar matsala, Majalisa ta fara gayyato mata Hukumar EFCC

- ‘Yan adawa a Majalisa sun bukaci ayi cikakken bincike a kan Hukumar NPA

- Hon. Ndudi Elumelu ya ce dakatar da Hadiza Bala Usman da aka yi, bai isa ba

- ‘Yan Majalisar suna zargin Ministan sufuri da kokarin lullube badakalar APC

Marasa rinaye a majalisar wakilan tarayya sun yi kira ga EFCC da sauran hukumomi da su ke da alhakin kama marasa gaskiya su yi bincike a kan aikin NPA.

‘Yan majalisar suna so a bibiyi zargin da ake yi na cewa hukumar NPA mai kula da tashoshin ruwan kasa ba ta dawo da N165bn cikin lalitar gwamnati ba.

Shugaban marasa rinaye a majalisar wakilai, Ndudi Elumelu, ya fitar da jawabi inda ya ce bai kamata a ce kwamiti ne kawai zai binciki wadannan zargin ba.

KU KARANTA: Ban da ikon bada kwangila a NPA - Bala Usman

Daiy Trust ta rahoto Honarabul Ndudi Elumelu ya na cewa zargin laifi mai nauyi irin wannan, ya na bukatar EFCC ta gudanar da binciken babu sani, babu sabo.

‘Yan majalisar hamayyar sun ce sun damu da yadda aka bar binciken zargin badakalar da ake tafka wa a hukumar NPA a hannun kwamitin je-ka-na-yi-ka.

“Siyasa ta shiga cikin binciken da ya kamata a gudanar domin a bankado mahukaciyar sata.”

Elumelu ya ce: “Muna zargin cewa zallar dakatarwar da aka yi wa shugabar NPA, Hadiza Bala Usman, da ake zargi da laifi, da kafa kwamitin bincike da Minista ya yi, ya na nufin gwamnatin da APC ta ke jagorata, tana rawa dumu-dumu a cikin rashin gaskiya.

Hadiza Bala Usman ta na cikin sabuwar matsala, Majalisa ta fara gayyato mata Hukumar EFCC
House of Reps Hoto: @NgrHouse
Asali: Twitter

KU KARANTA: ASUU: Ba a biya mu kudinmu ba, mu na bin albashin watanni 15

“Dauko kwamiti ya binciki zargin rashin gaskiya zai zama dabarar katange jami’an gwamnatin APC da aka samu da laifin facaka da kudi a NPA da wasu ma’aikatu."

‘Yan jam’iyyar hamayya a majalisar wakilan suna ganin kudin da aka wawura a NPA sun haura N165b.

“Muna kira ga EFCC ta yi maza ta bi ta kan Darekta Janar da ake zargi da laifi, Hadiza Bala Usman, ta soma bincikenta, da nufin daure ta idan har an same ta da laifi.”

A baya kun ji cewa an dakatar da shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwan Najeriya, Hadiza Bala Usman, domin bada damar gudanar da bincike a kan aikinta.

Wata wasikar da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya aikawa shugaban kasa, ya ce kudin da ya kamata ace NPA ta maida cikin asusun gwamnati sun gaza kima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng