El-Rufai: Na Fuskanci Tsangwama Daga Ƴar’Adua da Jonathan

El-Rufai: Na Fuskanci Tsangwama Daga Ƴar’Adua da Jonathan

- Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana yadda ya fuskanci tsangwama daga Yar'Adua da Jonathan

- Gwamnan ya ce tsoffafin shugabannin kasar na yi masa kallon cikas a tafiyarsu, abin da ya janyo masa tsangwama kwarai da gaske

- El-Rufai cikin hirar da aka yi da shi ya ce an dade ana masa kallon wanda ke son zama shugaban kasa hakan ke sa wasu ke masa kallon barazana

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi ikirarin cewa tsofaffin shugabannin kasar nan, Umaru Musa Yar'Adua da Goodluck Jonathan sun nuna masa tsangwama saboda suna masa kallon zai zame musu kalubale, rahoton Daily Trust.

A wata tattaunawa da ya yi da The Point, El-Rufai ya ce Yar'Adua ya wulakanta shi saboda ya yi tunanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo zai tsayar da shi takara, shi kuma Jonathan ya nuna masa tsangwama ne saboda yana kallon sa a matsayin wanda zai kawo masa cikas a neman tazarce.

El-Rufai: Na Fuskanci Tsangwama Daga Yar’Adua da Jonathan
El-Rufai: Na Fuskanci Tsangwama Daga Yar’Adua da Jonathan. Hoto: @GovKaduna
Asali: Facebook

Obasanjo ne shugaban Najeriya tsakanin 1999 zuwa 2007 kuma El-Rufai ne yayi masa ministan babban birnin tarayya Abuja.

Yar'Adua ne gwamnan Jihar Katsina lokacin Jonathan yana mataimakin gwamnan Jihar Bayelsa.

DUBA WANNAN: Kyauta Daga Allah: Wata Mata Ta Haifi Ƴan Tara a Morocco

Yar'Adua ya gaji kujerar Obasanjo da Jonathan a matsayin mataimakin shi. Bayan rasuwar Yar'Adua ranar 5 ga watan Mayu, 2010, Jonathan ya zama shugaban kasa.

A tattaunawar, El-Rufai yace Yar'Adua ne ya fara nuna masa tsangwama, Jonathan kuma ya ci gaba.

"Jonathan ya gamsu da ra'ayin sa cewa zan zamar masa matsala lokacin da zai nemi tazarce, dole ya sa na janye ko ta wane hali. A dalilin haka, Jonathan ya ci gaba da tsangwama min kamar yadda Yar'Adua ya fara."

"Ana ta alakanta ni da takarar shugabancin kasa, kamar yadda na fada, tun 2005, 2006, kusan shekara 15. Na sha wahala da wannan, an kore ni saboda haka kuma Jonathan ya yi yunkurin kai ni kurkuku.

KU KARANTA: Abun Al’ajabi: Wata Mata Da Bata San Tana Ɗauke Da Juna Biyu Ba Ta Haihu a Jirgin Sama

"Ana ta alakanta ni da takarar shugabancin kasa tun 2006, tun ina jagorantar babban birnin tarayya, Abuja.

Mutane na ta tsammanin shugaban kasa a wancan lokacin, Olusegun Obasanjo na shirin mika min mulki.

Yana cikin dalilan da suka sa aka kore ni.

Na jiki jikin marigayi shugaba Yar' Adua, cewa Obasanjo ya fitar da sunan yan takara biyu da za su gaje shi-sunan Yar'Adua da nawa. Kuma karya ne.

"Amma Yar'Adua ya yadda, kuma yake kallo na a matsayin barazana, kuma duk wani cece-kuce, karya da tsangwama da suka janyo aka kore ni daga kasar kusan wata 23 saboda wannan ne."

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164