Tallafin man fetur ya lashe N308bn cikin watanni uku a Najeriya

Tallafin man fetur ya lashe N308bn cikin watanni uku a Najeriya

Ci gaba da shigo ta tataccen man fetur daga kasashen ketare zuwa Najeriya, ya sanya kasar na narkar da makudan kudi wajen biyan kudin tallafin man fetur wanda a baya gwamnati ta so cire wa.

Bayan shigo da kimanin lita biliyan 5.61 daga waje zuwa Najeriya a rubu'i na biyu cikin shekarar 2019, kamfanin man fetur na kasa NNPC ya ce kasar ta malalar da kimanin Naira biliyan 308 wajen biyan tallafin man fetur cikin abinda bai wuci watanni uku ba.

Sabon rahoton da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar ya nuna cewa, an samu karuwar kaso 15.2 cikin 100 na adadin man fetur da aka shigo da shi Njaeriya a rubu'i na biyu cikin shekarar nan da muke ciki.'

Tun a shekarar 2017 ne kamfanin man fetur na kasa NNPC, ya kasance dillali daya tilo mai shigo da man fetur cikin kasar nan yayin da sauran 'yan kasuwa masu zaman kansu suka zame jiki a sanadiyar tsadar farashin man fetur dake shigowa a kan N145 na kowace lita daya.

'Yan kasuwar man fetur yayin zantawa da manema labarai sun yi hasashen cewa, akwai yiwuwar farashin saro lita guda ta man fetur zai kai kimanin N170 zuwa N200 sakamakon hawa da sauka da farashin ke yi a kasuwannin duniya.

KARANTA KUMA: Hatsarin mota ya hallaka mutane 11 a Zamfara

Lissafi zai kasance cewa, gwamnatin Najeriya za ta rika biyan Naira 55 na tallafi a kan farashin kowace lita guda ta man fetur muddin farashin sari ya kai Naira 200 da kamfanin NNPC ya kiyasta zai kai gabanin karshen shekarar 2019.

A shekarar 2015 da ta gabata gwamnonin da aka zaba karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya cire tallafin man fetur domin a cewar su hakan zai basu dama ta bunkasa tattalin arzikin kasa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel