Karfa-karfa: Buhari da Ministansa, Amaechi sun saba doka wajen dakatar da Hadiza Bala Usman

Karfa-karfa: Buhari da Ministansa, Amaechi sun saba doka wajen dakatar da Hadiza Bala Usman

- Gwamnatin Tarayya ba ta bi ka’ida wajen dakatar da Hadiza Bala Usman ba

- A doka ya kamata a sanar da shugabar NPA laifin da ake zargin ta da aikatawa

- Ba a ji ta bakin Bala Usman ba, sai kawai aka yi waje da ita, aka soma bincike

Ba a sanar da shugabar NPA, Hadiza Bala Usman game da laifin da ake zargin ta da yi ba, kuma ba a aika mata wata takardar sammaci kafin dakatar da ita ba.

Jaridar Premium Times ta samu labari cewa ba a bi doka wajen dakatar da Hadiza Bala Usman daga kujerar da ta ke kai na babbar darektar hukumar NPA ba.

Har zuwa yanzu, Bala Usman ba ta san laifin da ake tuhumar ta da shi ba, domin fadar shugaban kasa ba ta aika mata da wata takarda a kan wannan magana ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dakatar da Hadiza Bala Usman daga kujerar NPA

Da aka tuntubi shugabar ta NPA, ta bayyana cewa ba ta san laifin da ta yi ba. A dokar kasa, sai an bi wadannan matakai kafin a iya sauke mutum daga kan kujera.

Sallama ko dakatar da shugaban ma’aikata daga mukaminsa ba tare da an sanar da shi laifinsa domin ya kare kansa ba, ya saba doka da tsarin aikin gwamnati.

A wata sanarwa da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya fitar a 2020, ya tabbatar da wannan doka, ya ce sai an yi bincike kafin a dauki wani mataki.

Amma a lamarin shugabar hukumar NPA, duk an tsallake wadannan matakai da gwamnatin tarayya ta sa da kanta, aka zarce kai-tsaye, aka hukunta Usman.

KU KARANTA: Za a binciki aikin da Bala Usman ta yi a NPA - Buhari

Karfa-karfa: Buhari da Ministansa, Amaechi sun saba doka wajen dakatar da Hadiza Bala Usman
Shugaban kasa da Hadiza Bala Usman Hoto: www.dailypost.ng
Asali: UGC

‘Yan jarida sun nemi jin ta bakin shugaban majalisar da ke sa ido a kan aikin hukumar NPA, Jide Adesoye, amma sam ba a iya samunsa ta layin wayar salularsa ba.

A ka’ida, Jide Adesoye da majalisar sa ne za su binciki Bala Usman, su kuma bukaci ta kare kanta daga zargi, bayan nan sai a sanar da Minista matakin da za a dauka.

Ana zargin cewa harkar kwangila ce ta hada shugabar NPA fada da mai gidanta, Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda shi kuma ya ba manya shawarar a sauke ta.

Kafin yanzu kun ji cewa jigon PDP a jihar Legas, Bode George ya na ganin ya kamata hukumar EFCC ta yi ram da Bola Tinubu, ta binciki kamfaninsa na Alpha Beta.

Bode George ya ce rainin wayau ne ace irinsu Tinubu ne ke neman kujerar Shugaban kasa, ya ce idan abokin hamayyarsa ya samu mulki, ya tashi daga 'dan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel