Daliban Afaka 37: Na yi barin juna biyu a hannun yan bindiga, cewar Fatima

Daliban Afaka 37: Na yi barin juna biyu a hannun yan bindiga, cewar Fatima

- Daliban Afaka na bayyana abubuwan da suka fuskanta cikin kwanaki 56 da suka a daji

- Akwai matar aure guda da tayi rashin juna biyu da kuma mahaifinta a lokacin

- Ta jaddada cewa yan bindigan basu yi musu fyade ba

Wata daliba mai juna biyu cikin matan da yan bindiga suka sace a makarantar fasahar Gandun Daji dake Afaka, Fatima Ibrahim Shamaki, ta bayyana yadda tayi bari a hannun yan bindiga.

A ranar Laraba, kwanaki 56 bayan sacesu, an saki sauran dalibai 27 dake hannun yan bindigan ranar Laraba.

Asali dalibai 38 yan bindigan suka sace daga makarantar amma daya ya samu kubuta.

Daga baya kuma yan bindigan suka saki 10 bayan biyansu kudi don fansan dukkan daliban.

Yayin hira da Daily Trust bayan sakesu, Fatima Ibrahim Shamaki, tace tana dauke da cikin watanni biyu lokacin da aka sacesu.

Ta bayyana cewa ta yi barin cikin sakamakon wahala.

KU KARANTA: An biya N15m kuma an saki kasurgumin dan bindiga 1 a matsayin fansan daliban Afaka 27

Daliban Afaka 37: Na yi barin juna biyu a hannun yan bindiga, cewar Fatima
Daliban Afaka 37: Na yi barin juna biyu a hannun yan bindiga, cewar Fatima Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA NAN: Mun shawo kan yan bindiga da suka sace daliban Greenfield, ba zasu kashesu ba: Sheikh Gumi

Fatima, ta ce yan bindigan basu san tana da ciki ba, duk da cewa suna yawan tambaya idan akwai mai juna biyu cikinsu.

Ta ce ta boye hakan ne saboda tsoron kada su cutar da ita saboda suna barazana ga marasa lafiya

"Ina tsoro saboda duk lokacin da wasu cikinmu suka ce basu da lafiya, suna cewa zasu kashe mutum. Shi yasa nayi tunanin idan na fada musu halin da nike ciki zasu kasheni," tace.

"Sauran kawaye na suka taimaka min lokacin. Muna taimakawa juna lokacin jinin al'ada."

Bayan barin da tayi, Fatima ta yi rashin mahaifinta, Ibrahim Shamaki, lokacin da aka sace su.

A cewar wata dalibar, Sarah Sunday, ta ce sun shiga wani irin mugun hali, inda ko wanka ba'a amince musu sun yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel